131012-labarin-gimbiyar-dawisu-Lubabatu
|
Irin rawar da ake kira rawar dawisu rawar gargajiya ce ta kabilar Dai. Bisa ga al'adar kabilar Dai, dawisu tsuntsu ne da ke kawo albarka da alheri. Amma a game da asalin rawar, akwai wata almara da ke nuna cewa, a shekaru sama da dubu da suka wuce, wani babban jagoran kabilar Dai ya kwaikwayi yadda dawisu ke tsayawa da kuma tafiya, har ya kirkiro rawar dawisu ta ainihi. Daga bisani, 'yan kabilar sun yi ta kara kyautata rawar, kuma rawar dawisu ta kara samun farin jini sosai ga 'yan kabilar. A lokacin bukukuwa, 'yan kabilar Dai su kan taru, su buga gangunansu na gargajiya da suke kira kafafuwan giwa (bisa ga sifar gangunan), kuma su fara raye-rayen dawisu.
shirinmu na yau zai ajiye kayansa kan wata 'yar rawa da ta sadaukar da rayuwarta ga rawar dawisu, wadda ake mata kirarin gimbiyar dawisu.