130927-Ziyara-zuwa-birnin-Dongxing-da-aka-samu-jamaa-masu-tsawon-rayuwa-a-kasar-Sin-Lubabatu
|
Sinawa kan ce, "da wuya a samu icen da ke da shekaru dubu, haka kuma da wuya a samu mutumin da shekarunsa ya kai 100". Amma akwai wani birni mai suna Dongxing a jihar Guangxi da ke kudancin kasar Sin, wanda ake daukarsa a matsayin gari na mutane masu tsawon rayuwa, har ma kwanan baya, yayin da wani wakilin CRI ke ziyara a garin, ya gamu da wani tsoho dan kabilar Jing mai suna Ruan Zhongjie, wanda aka yi masa bikin murnar cika shekaru 103 da ranar haihuwarsa.