131009-dole-ne-mu-kula-da-tsofaffi-Sanusi
|
Wannan rana ce ta musamman ga tsofaffi ko mazan jiya a duk fadin duniya, inda bayanai suka nuna cewa, gwamnatoci a wasu kasashe kan shirya bukukuwa tare da gabatar da jawabai, a wasu lokutan ma a kan gabatar da shirye-shirye a gidan redoyi da Talabijin har ma a kan wallafa bayanai ko sharhi a jaridu kan batutuwan da suka shafi tsofaffi game da irin nasarorin da suka cimma ko gudummawar da suka bayar ga ci gaban kasa ko al'umma.
A ranar 14 ga watan Disamban shekarar 1990 ne, babban zauren majalisar dinkin duniya, ya ayyana ranar 1 ga watan Oktoban kowa ce shekara a matsayin ranar martaba tsofaffi ta duniya, sannan aka yi bikin farko na wannan rana a fadin duniya a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1991.
Tun wannan lokaci ne kuma, aka ci gaba da martaba wannan rana a duk fadin duniya, ganin irin rawar da wadannan bayin allah suka bayar ga ci gaban al'amura a wannan duniya tamu. Wannan ya sa masana ke ganin cewa,akwai bukatar mahukunta su bullo da matakai da za su inganta rayuwar tsofaffi daga dukkan fannoni, saboda rawar da suka taka wajen shimfida makomar da kasashen da yanzu al'ummominsu ke cin gajiya. (Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)