130919-Bikin-haduwa-da-iyalai-ta-Sinawa-lubabatu
|
Bikin Zhongqiu na daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya na kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiranta bikin Zhongqiu, wato bikin tsakiyar yanayin kaka. A wannan rana, wata ya kan cika, kuma ya fi da'ira da kuma haske, kuma a lokacin da jama'a ke hango duniyar wata, su kan fara kewan iyalansu, shi ya sa Sinawa sun dauki bikin a matsayin bikin haduwar iyali. Don haka, a yayin bikin, Sinawa a duk inda suke, in sun ga dama, su kan koma gida don haduwa da iyalai.
Ita dai wannan rana ta haduwa da iyalai ta kasar Sin nada dogon tarihi, kuma in an yi bincike, za a gano cewa, bikin ya samo asalinsa ne daga ibada da sarakunan gargajiya a kasar Sin suka gudanar, wadanda su kan ba da ibada ga duniyar rana a lokacin bazara, kuma a lokacin kaka, su kan ba da ibada ga duniyar wata, sai daga bisani, wannan al'ada ta yi ruwan dare a tsakanin jama'a, har ma sannu a hankali ya zama wani bikin da jama'a su kan yi.
Abubuwan da a kan yi a yayin bikin Zhongqiu sun hada da kallon wata da kuma cin wainar wata. A yayin wannan salla, iyalai da 'yan uwa da abokan arziki na haduwa wuri guda a filin gida domin kallon hasken wata, ana hira kuma ana cin wainar wata da 'yayan itatuwa cikin annashuwa da jin dadi.Wani abin da ba a iya rasa shi ba a yayin bikin Zhongqiu shi ne wainar wata, abincin da shi ma ya samo asalinsa daga abincin da aka yi domin ibada ga wata. Akasarin wa'inar wata a kan yi shi da'ira, wanda ya kasance alama ce ta haduwa da iyali.
Bikin ranar haduwa da iyali na bambanta daga wasu yankuna zuwa wasu yankuna, amma kuma buri guda ne shi ne na samun makoma mai kyau. (Lubabatu)