130828-RANAR MATASA-TA DUNIYA-Sanusi.m4a
|
Ranar matasa ta duniya, ko "International Youth Day" a turance, rana ce da MDD ta kebe musamman domin fadakarwa, da wayar da kan al'umma kan muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar matasa, a duk inda suke a fadin wannan duniya.
Kamar sauran muhimman al'amura da MDD ta kebewa ranaku na musamman, ita ma wannan rana ta matasa, ana gudanar da bikin tunawa da ita ne a ranar 12 ga watan Agustan kowa ce shekara, Kamar yadda ke kunshe cikin tanadin wani kudurin majalisar na shekarar 1999.
Galibi a wannan rana, gwamnatoci a matakai daban-daban,kungiyoyi da hukumomi masu zaman kansu, na yin nazari da shirya tarukan wayar da kai, kan batutuwan da suka shafi rayuwar matasa.baya ga bukukuwan al'adu, da tarukan karawa juna sani, tare da gabatar da makalu domin tunawa da wannan rana.
Alkaluma na nuna cewa, matasa na daukar kaso mafi yawa a cikin alu'umma,wannan yasa ake nazarin irin tasiri, da ci gaba, tare da kalubalen da hakan ke haifarwa ga rayuwar matasan. A hannu guda kuma ake nazartar irin gudummawar da matasa, har ma wadannda suka kasance 'yan ci rani ke baiwa yankunan da suka kaura,duk da tarin matsalolin da hadarin da suke shiga a kokarin biyan bukatunsu .
Don haka,masu fashin baki na ganin cewa, kamata ya yi gwamnatoci su yi kokarin samar wa matasa ayyukan yi,yayin da suma matasan ya kamata su tashi tsaye don bayar tasu gudummawar ta yadda haka za ta cimma ruwa(Ibrahim/Saminu/Sanusi Chen)