130708-Dr-Asmau-Sani-Maikudi-1-bilkisu
|
Ita ce wata malamar makaranta, Uwa wadda neman ilimi ya zama mata wani tsani na cigaba a rayuwa a dukkan fannoni na rayuwar ta, kama daga Iyalinta zuwa harkokin rayuwa na yau da kullum.
Dr Asma'u Sani Maikudi ta fara koyar wa ne tun daga makarantar sakandare har zuwa yanzu, inda take ci gaba da koyarwa a makarantar kimiyayya da fasaha ta gwamnatin tarayya wato Kaduna polytechnic dake garin Kaduna, ta kuma yi mana bayanin yadda tun farko ta tsinci kanta a wannan fanni na malanta da kuma nasarorin da ta samu a sakamakon ILIMI, wanda idan kuka biyo mu a sannu cikin wannan shirin za ku ji bayanan da ta yi game da muhimmancin ilimi musamman ga 'ya'ya mata, sannin kowa ne cewa, ilimi shi ni gishirin zaman duniya kuma ginshikin cigaban al'umma a ko ina suke a duniyan nan…