130830-rigar-Qipao-ta-matan -sinawa-lubabatu.m4a
|
Rigar Qipao na daya daga cikin salon kayan jiki na matan Sinawa, wadda riga ce ta gargajiya da ke da wani tsawon tarihi na shekaru 300. A hakika rigar Qipao ta samo asalinta daga rigar gargajiya ta matan kabilar Man ta kasar, sai dai a farkon karni na 20, an kawo wasu gyare-gyare ga irin rigar matan kabilar Man, har aka fito da wani sabon salon rigar da ta samu karbuwa sosai tsakanin mata, rigar da muka sani da Qipao ke nan. Sakamakon yadda rigar Qipao ke iya nuna kyaun hali na mata, an kuma dauke ta a matsayin rigar biki ga matan kasar.
Rigar Qipao wata rigar gargajiya ce da a kan dinka da siliki, Linen, sai dai a lokacin zamani, an kuma fara yin amfani da wasu yadi na zamani wajen dinkin Qipao. In an lura kuma, za a ga akwai launuka iri iri ga rigar Qipao, sa'an nan a kan yi zane-zane iri iri a kan rigar Qipao, ciki har da furanni, tsuntsaye, dabbobi da sauran alamu na fatan alheri. Rigar Qipao tana da karamar kwala, kuma ana sanya wa rigar wasu maballe a kaikaice daga kwalar rigar zuwa hammata ta yadda za a samu saukin sanyawa da kuma cire rigar baya ga karawa rigar ado. Galibin tsawon rigar a zamanin da ya kan kai har zuwa idon sawu sannan ana yi mata dan tsagu zuwa gwiwa, sai dai rigunan Qipao suna tafiya tare da zamani, wadanda a yanzu akwai irin rigunan da ake dinka su zuwa gwiwa. Sa'an nan, a da a kan yi rigar mai dogon hannu, amma yanzu haka ma akwai masu dogayen hannu da gajerun hannu.(Lubabatu)