130816-Hajiya-Inna-Maryam-Ciroma-Kande.m4a
|
Wannan filin namu na In Ba Ku Ba Gida yayi nasarar zantawa da wata tsohuwar ministar harkokin mata a tarayyar Nigeriya, tsohuwar shugabar mata ta kasa baki daya a jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriya, har ila yau sannan kuma ta taba yin takarar kujerar majalissar dattijai a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, wannan muhimmiyar bakuwa ita ce Hajiya Inna Maryam Ciroma.
Hajiya Inna Maryam Ciroma, fitacciyar mace ce a gwagwarmaya da kuma ayyukan da suka shafi rayuwar mata, musamman ma a fannin da ta fi iyawa wato siyasa, abin da yasa wannan fili ya bukaci tayi ma masu sauraro bayani game da abubuwan da suka fi damun mata a nata fahimta, da kuma kalubalolin da mata suke fuskanta, sannan kuma mene ne ra'ayinta a kan ko akwai hanyar da matan za su iya bi nan gaba domin ganin cewa lalle an dama da su a kowane fannin yadda ya kamata? Sannan kuma mene ne shawararta ga mata da matasa?
Masu sauraro ga yadda hirar tamu ta kasance da fatan za'a amfana daga bayananta.