130807-Sin-da-Afirka-na-moriyar-juna-Sanusi
|
Sai dai duk da wannan rashin fahimta da irin wadannan kasashen ke yi wa wannan dangantaka dake tsakanin Sin da Afirka, shugabannin kasar Sin sun jaddada cewa, babban tushen dake tsakanin Sin da Afirka ba zai canja ba.
Alkaluma sun nuna irin tallafi da moriyar da kasashen Afirka suka samu daga wannan dangantaka a bangarori daban-daban kamar su al'adu, ilmi, makamashi, sufuri, tattalin arziki, kiwon lafiya, fasahohin aikin gona da dai sauransu.
Misali na baya-bayan nan, shi ne bashi da tarin yarjeniyoyin da Najeriya ta kulla da gwamnatin kasar Sin yayin ziyarar da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kawo kasar Sin a watan Yulin shekarar 2013.
Saboda muhimmancin wannan dangantaka tsakanin bangarorin biyu, har ta kai ga kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, abin dake kara nuna karfafa wannan dangantaka mai tarin alheri ga sassan biyu.
Daga karshe masu fashin baki na cewa, muddin ana bukatar cin gajiyar wannan dangantaka yadda ya kamata, wajibi ne bangarori biyu su mutunta alkawuran da suka cimma, mutunta juna, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a bangarori gwamnatoci da al'ummomin sassan biyu. (Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)