in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko kungiyar Hezbullah ta Lebanon kungiya ce ta nuna ta'addanci?
2013-08-02 14:01:48 cri

An kafa kungiyar Hezbullah ce tun yakin da aka gwabza tsakanin Isra'ila da kasar Lebanon, inda malaman addinin Islama a yankin suka yi tunanin kafa kungiyar da nufin kare muradun kasar ta Lebanon da sauran sassan kasashen Larabawa, kuma an kafa ta ne a hukumance a shekara ta 1985.

Manufofin kungiyar sun hada da tabbatar da ikon yankunan kasar Lebanon da wasu sassan kasashen Larabawa har ma da kasashen musulmai da ke bukatar tallafin kungiyar.

Bayanai sun nuna cewa, kasar Lebanon ce take baiwa kungiyar ta Hezbullah taimako a siyansce, yayin da kasar Iran ke baiwa kungiyar tallafin kudi, horo, makamai da makamantansu. Ana iya kallon kungiyar a matsayin kungiyar masu fafutuka ko kuma jam'iyyar siyasa wadda ke da kujeru da dama a majalisar dokokin kasar Lebanon.

Irin ayyukan yakin sari-ka-noke da kungiyar ke gudanarwa, ya sa kungiyar EU a baya-bayan nan ta dauki matakin sanya ta cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda a duniya, duk da cewa babu wata alaka ko hulda tsakanin kungiyar da kasashen EU.

Bayanai sun nuna cewa, kasancewar kungiyar, wata babbar barazana ce ga dorewar kasar Isra'ila, wannan ya sa kasar Amurka da kawayenta sun dauki wannan mataki, abin da masu sharhi ke cewa, manufar daukar wannan mataki kan kungiyar ta Hezbollah, ita ce rage karfin kungiyar ta fuskar tattalin arziki, kuma matakin da ake cewa ba zai yi wani tasiri ba.

Sai dai shugabannin kasashen Iran da Lebanon sun bayyna cewa, matakin ba zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ba kuma ba zai canja manufa da tasirin kungiyar ba. (Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China