130726-rayuwar-chinua-achebe-1-Lubabatu
|
An haifi Farfesa Chinua Achebe ranar 16 ga watan Nuwambar shekarar 1930, a garin Ogidi na Jihar Anambra, dake Kudu maso Gabashin Najeriya. Dan asalin kabilar Igbo ne, kuma cikakken sunansa shi ne Isaiah Okafor Achebe. Saboda shaharar da ya yi ta fuskar rubutu a fannin adabi, ake masa lakabi da "uwa-uba a fannin adabi a nahiyar Afrika".
Shekaru 5 kacal da haihuwarsa Chinua Achebe ya fara cudanya da kiristoci 'yan mishan, da kuma malaman addinin yankin da yake, kuma ko da yake a makarantar firamare da farko-farko ya rika daukar darussansa ne da yaren Igbo, daga baya yayin da ya kai shekaru 8 da haihuwa, sai ya fara koyon harshen Turanci.
Tarihi ya nuna yadda Achebe ya dage haikan wajen karance-karance, lamarin da ya sanya shi yin fice a tsakanin ragowar dalibai tsaransa. Yayin da ya cika shekaru 14, ya samu shiga makarantar kwalejin gwamnati dake garin Umuahia, ya kuma kammala wannan makaranta tare da shahararren mawakin adabin nan mai suna Christopher okigbo. Kuma ko da yake ya samu kudaden tallafi da ake baiwa dalibai domin karatun likitanci a jami'ar Ibadan, shekara daya da fara wannan karatu, Achebe ya sauya sheka zuwa sashen nazarin adabin harshen Turanci, inda ya kasance abokin karatun shahararren marubucin adabin nan da ya samu lambar yabo ta Adabi wato Farfesa Wole Soyinka. Littafinsa da ake kira da "Girls at War" na cikin na farko-farko, dake kunshe da labarai da ya rubuta yana dalibin jami'a a shekarar 1972.
Manyan rubuce-rubucen Chinua Achebe sun hada da"Things Fall Apart", "Anthills of the Savannah", "Arrow of God", "A Man of the People", da sauransu.
Masu fashin baki dai a fannin rubuce-rubuce musamman ma na adabi, na bayyana cewa, Achebe ya bada gudummawa mai tarin yawa ga ci gaban rayuwar al'ummar Afirka, kuma rasuwarsa ta bar wani gibi mai girma, da za a dade kafin a cike shi, musamman a sassa, da yankunan nahiyar Afirka.
Achebe ya samu lambobin yabo da suka hada da na "Man Booker International Prize a shekarar 2007, da "the Dorothy and Lillian Gish Prize" a shekarar 2010. Ya kuma samu digirin girmamawa daban daban, daga jami'oi kimanin 30 a sassan duniyan nan.
A ranar 21 ga watan Maris na wannan shekara ta 2013, Chinua Achebe ya rasu a birnin Boston, kasar Amurka, ya mutu yana da shekaru 82 da haihuwa. A kuma ranar 23 ga watan Mayu, an gudanar da bikin jana'izarsa a garinsa da ke jihar Anambar, kuma manyan shugabannin da suka hada da shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan da takwaransa na kasar Ghana John Dramani Mahama suka halarci bikin.(Lubabatu)