To, galibin wadannan cibiyoyi ko kungiyoyi suna zaman kansu ne, wato ba na gwamnati ba ne, iyakacin dai za'a iya cewa ita gwamnatin ta san da zamansu. To daya daga cikin irin wadannan kungiyoyi ita ce Service to Humanity Foundation, a jihar Katsina dake arewacin Nigeriya, wadda uwargidan Gwamnan jihar Hajiya Fatima Ibrahim Shema ta kafa ta musamman domin taimaka ma yara masu fama da lalurar amosanin jini wato sickle cell a turance.
Filinmu na "In Ba Ku Ba gida" ya nemi wannan bakuwa tamu ta musamman domin ta fada ma masu sauraro ayyukan wannan kungiya tata, da fatan zaku kasance tare da mu.
130626-Hajiya-Fatima-Ibrahim-Shema-Kande
|