in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ibrahim a garin Yiwu
2013-07-09 09:14:03 cri

Cikin 'yan shekarun nan, sakamakon bunkasuwar harkokin tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, mutane da yawa daga kasashen Afirka sun zo nan kasar Sin don yin aikin cinikayya ko karatu. Alhaji Ibrahim, wani dan kasuwa ne na Nijeriya, yana daya daga cikinsu, kuma yau shekaru 15 ke nan yana zama a garin Yiwu da ke kudancin kasar Sin.

"Ina son Ximilu, gudu daya. Wannan, guda daya."

"Guda daya, shi ke nan?"

"Shi ke nan."

Masu sauraro, yadda malam Ibrahim ke yin odan abinci da Sinanci a wani dakin cin abinci na Musulmi da ke wurin cinikayyar kasa da kasa na garin Yiwu ke nan. Ibrahim bai taba shiga makaranta don koyon sinanci ba, amma kamar yadda ya nuna mana cewa, zamansa a garin Yiwu na shekaru sha biyar ya sa har ya zama tamkar basine.

Malam Ibrahim ya ce, kafin ya zo kasar Sin, ya taba yin kasuwanci a jihar Kano da ke arewacin kasar Nijeriya, amma sabo da wasu matsalolin da ya gamu da su da suka hada da karancin wutar lantarki, tabarbarewar yanayin cinikayya da na tsaro da dai sauransu, ya shiga mawuyacin hali wajen ci gaba da tafiyar da harkokin cinikayyarsa. Sai dai daga baya, Allah ya kawo shi garin Yiwu na kasar Sin tare da abokansa, inda bai yi zaton samun damar ci gaba da kasuwancinsa ba, Ya ce,"Ina zuwa dai ina yin ciniki daga shekara 15 ina zuwa, amma yanzu kamar daga shekara 3 shi ne na zauna nake yin harkoki a nan, ina yin sarka kyalle, ina yin mayafi, ana yin cinikayyar hula da dai sauran abubuwan da yadda ya kamata, harkokin ciniki ana tabawa, ina nan ina taimakon mutane al'ummata, suna zuwa ana sayan kaya ana tura musu da kayansu, kuma Alhamdulillahi yanzu Allah ya sa kuma na fara nawa harkokin. Muhimmanci da addinina da kuma al'ummata da kuma ni ma da iyalan nawa, albarka abin da Allah ya sa za mu samu na halal mu je mu ma mu ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci mu ma a kasarmu. "

Malam Ibrahim na daya daga cikin 'yan Afirka da suka fara zuwa garin Yiwu, kuma ba shakka ya cimma nasara a garin. A halin yanzu, 'yan kasahen katare kimanin dubu dari uku da tamanin na zuwa garin Yiwu, a yayin da dubu tamanin daga cikinsu suka zo daga kasashen Afirka. Cikin 'yan shekarun nan, irin cudanyar da ke tsakanin jama'ar kasar Sin da kasashen Afirka na ba da gudummawa sosai wajen inganta dangantaka da hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

Yayin da yake magana kan dalilan da suka sa ci gaban harkokin hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, malam Ibrahim ya nuna cewa, a garin Yiwu, Sinawa suna kaunar baki suna karrama su, wannan shi ne babban dalilin da ya sa mutanen waje suke son zuwa, su zauna su yi aiki a nan tare kuma da dukufa wajen cimma burinsu a nan. Ya ce, "Abubuwa da yawa, mu kaman musulmi abin da ya fi burge mu, shi ne abin da ya shafi addini, cewa an kyale mu muna gudanar da abin da ya shafi harkar addininmu, babu wata takurawa ko matsala, Ana kyale mu muna yin addininmu lafiya kalau. Akwai wuraren salla, masallatai sun fi guda 20, ni dai yawan wadanda na sani, kaga ga shi akwai babban masallacin Jumma'a a nan, akwai masallatai da yawa."(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China