in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yada al'adu da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya
2013-07-08 15:52:21 cri

A ranar Jumma'a 15 ga watan Yuni ne, ministan al'adu na kasar Nijeriya Edem Duke ya kai ziyara birnin Chengdu da ke kasar Sin, inda ya halarci bikin tunawa da abubuwan tarihi da aka gada daga kaka da kakanni da ba su shafi kayayyaki ba, kuma ya gana da takwaransa na kasar Sin Wato Mista Cai Wu, a yayin ganawarsu, Mista Cai Wu ya jinjina wa Mista Edem Duke bisa kokarinsa don yada dankon zumunci da karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ta fuskar al'adu.

A nasa bangare kuma, Minista Duke ya nuna godiya ga ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta Sin, sabo da kokarinta na yada dankon zumunci a tsakanin kasashen Sin da Nijeriya. Yana mai cewa, a daidai lokacin zuwansa a kasar Sin, wato kafin ziyarar shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan a kasar Sin, yana fatan yin amfani da ziyararsa, don sa kaimi ga shugaban kasar Nijeriya ya mayar da harkokin al'adu wani muhimmin bangare cikin ziyararsa a kasar Sin. Nijeriya ita ma, za ta koyi fasahohi daga kasar Sin, wajen mayar da al'adu wani muhimmin bangare cikin aikin raya kasar, kuma tana fatan inganta mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin a fannin al'adu da sauransu.

Haka kuma, yayin da Ministan Edem Duke ke yin ziyara a kasar Sin, wakilinmu ya samu damar zantawa da shi, yayin da ya bayyana dalilin da ya sa ya dora muhimmanci sosai game da mu'amalar al'adu da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya, yana mai cewa, Kasar Sin babbar kasa ce da ke da daddaden tarihi a duniya, haka ma, tana da al'umma mafi yawa a duniya. Ban da wannan kuma, kasar Nijeriya ita ma, babbar kasa ce da ke da yawan al'umma a nahiyar Afrika, inda aka lakaba mata suna cibiyar al'adu ta kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, sabo da haka, inganta mu'amalar al'adu da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya yana da muhimmanci kwarai da gaske. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa shekarar 2050, yawan al'ummar da ke kasar Nijeriya zai dau matsayi na uku a duniya, wato bayan kasashen Sin da India. Sabo da haka ne, mu'amalar al'adu zai kawar da duk wani shigen da ke kasancewa tsakanin bambancin al'adu na kasashen Sin da Nijeriya, kuma inganta mu'amalar al'adu da jama'a tsakanin kasashen biyu na da muhimmanci kwarai da gaske."

A cikin 'yan shekarun nan, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da habaka, kuma jama'ar kasar Sin sun kara mai da hankali sosai game da raya al'adu, haka kuma abin da ya nuna cewa, an ci gaba da raya kasar Sin. Sabo da Nijeriya za ta koyi fasahohi daga kasar Sin wajen mayar da al'adu don ya zama wani muhimmin sashi cikin aikin samun ci gaba cikin dogon lokaci, haka kuma, a matsayin wata alamar yin mu'amalar al'adu da ke tsakanin kasar Sin da ta Nijeriya, Nijeriya ta zama kasa daya tilo daga cikin kasashen Afrika wadda ta kafa cibiyar al'adu a kasar Sin, kuma kasar Sin ita ma, kwanan baya, ta yanke shawara cewa, za ta kafa cibiyar al'adu a kasar Nijeriya. Minista Duke ya yi imani cewa, a karkashin babban tushen yin mu'amalar al'adu da ke tsakanin kasashen nan biyu, aikin yin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya zai kara karfafuwa.

Yayin da minista Duke ya bayyana matakan da za a dauka wajen yada al'adu a kasar Sin da kasashen duniya, ya ce, Matsayin kasar Nijeriya a kasashen Afrika, ya yi daidai da matsayin kasar Sin a kasashen duniya. Duk inda mutum ya je a duniya da ka je, akwai Sinawa a wurin, haka ita ma Nijeriya ta zama tamkar haka. A halin da muke ciki yanzu, a ko wace shekara, akwai Sinawa da yawansu ya kai miliyan 6 da su kan yi tattaki zuwa kasashen waje, amma wasu manyan kasashen yammacin duniya ba su son fita zuwa sauran kasashe, wannan ya nuna wayewar kai da ci gaba na kasar. Amma abin da ya fi damun kasar Sin shi ne, ba ko wane basine ne zai samu damar zuwa Nijeriya ba, haka kuma bude cibiyar al'adu ta Nijeriya a kasar Sin zai kara saniya jama'ar Sinawa da dukkan al'ummar kasashen Asiya sanin al'adun Nijeriya, kuma cibiyar al'adu ta Nijeriya ta samar da wani dandali ga Sin. Ban da wannan kuma, Mista Edem Duke ya bayyna cewa, a bana, Nijeriya za ta ci gaba da kafa cibiyar al'adunta a kasar Trinidad and Tobago da birnin Johannesburg dake kasar Afrika ta Kudu, ta yadda jama'ar kasashen duniya za su kara fahimtar Nijeriya.(bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China