in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin CCECC na kasar Sin yayi bikin kaddamar da layin dogo da ya hada Abuja da Kaduna
2013-07-05 17:19:08 cri

Ranar Alhamis 4 ga wata ne, a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, katafaren kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna CCECC yayi bikin kaddamar da shimfida layin dogon da ya hada birnin Abuja da kuma jihar Kaduna, inda mataimakin shugaban kasa Alhaji Mohammed Namadi Sambo ya nuna babban yabo ga lamarin. Ga cikakken rahoton da wakilinmu Murtala ya aiko mana.

An yi wannan gagarumin buki ne a harabar masana'antu ta Idu dake birnin Abuja, wato Idu Industrial Zone a turance. Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Alhaji. Mohammed Namadi Sambo, ministan kula da harkokin zirga-zirga Senata Umar Idris, babban manajan kamfanin CCECC reshen Najeriya Mista Shi Hongbing da sauran manyan jami'ai suka halarci bikin.

Layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna, layin dogo ne na zamani da ya kasance na farko da kamfanin CCECC na kasar Sin ya ba da taimako wajen shimfidawa. Layin dogon zai ratsa ta birnin Abuja, jihar Niger, da kuma jihar Kaduna. An ce, bayan da aka fara zirga-zirgar jirgin kasa a kan wannan layin dogo, daga Abuja zuwa Kaduna za'a shafe awa daya ne kacal, kuma za'a sassauta matsalar cunkoson motoci a kan hanyoyin da suka hada da Abuja, jihar Niger da kuma jihar Kaduna.

Samar da guraben ayyukan yi ga jama'a, shi ma daya daga cikin muhimmiyar rawar da layin dogon da ya hada Abuja da jihar Kaduna ke takawa. Game da wannan batu, babban manajan kamfanin CCECC reshen Najeriya Mista Shi Hongbing ya bayyana cewa: "Kawo yanzu, mun yi hayar ma'aikata 'yan Najeriya sama da dubu 4 don su gudanar da aikin shimfida wannan layin dogo. Kuma da muka idan muka fara zirga-zirgar jiragen kasa, za mu kara samar da horo da yin hayar ma'aikata 'yan Najeriya sama da dubu 5."

Bisa labarin da muka samu, an ce, layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna, tsawonsa ya kai kilomita kusan 187 ne, kuma za'a kammala dukkan aikin a karshen shekara mai zuwa.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China