130703salisudawanau01
|
A shekarar 2012, an samu nasarar tafiyar da aikin "Kyan surar jihar Xinjiang", inda masu karatu na gida da na wajen kasar Sin suka tsokane kwarakwatan idanu da hotunan dake bayyana ni'imtattun wurare na jihar Xinjiang, tare da jefa kuri'a domin zaben hotunan da suka fi so,da ba da sharhi a kansu ta hanyar yin amfani da IPAD da wayar salula da dai sauransu, a kokarin kasancewa cikin wannan aiki. Yanzu Salisu Dawanau da ya fito daga Abuja, Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya ya samu nasara a cikin wannan gasar kacici-kacici, ya samu damar ziyartar jihar ta Xinjiang. Mene ne ra'ayinsa game da jihar Xinjiang? Bari mu kara fahimta!