in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarin wani manomi da ke noman furanni
2013-07-19 16:53:18 cri


A yankin Dounan na birnin Kunming, hedkwatar lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, akwai wata babbar kasuwar cinikin furanni da ta kasance mafi girma a nahiyar Asiya, inda kowace rana da sassafe, sai ake tarar da cunkuson mutane tare da wucewar motoci masu dauke da furanni a ciki, a yayin da 'yan kasuwa ke kokarin yanyanka furanninsu suna ajiye su tari tari. Tarin nau'o'in furanni na Rose, Lily, carnation da sauransu, masu launin ja, rawaya, fari da kuma ruwan hoda, kai sai ka ce wani teku ne mai cike da nau'o'in furanni daban daban. Amma kada ku yi zaton wannan ne lokacin da hada hadar saye da sayarwa tafi habaka a wannan kasuwa, sabo da cinikin kiri ne ake fi yi a rana. A hakika, idan ka zo nan da daddare, kasuwar za ta fi burge ka da irin hada-hadar saye da sayarwa, inda kowace rana da dare, tun daga karfe 11 har zuwa karfe takwas na safiyar kashegari, 'yan sari da kuma dillalan furanni suke haduwa a nan suna ciniki.

A yanzu haka, kusan babu wanda bai san sunan Zhang Yuelong ba idan an ambaci batun noman furen Carnation a wurin, wanda yake da gonar da fadinta ya kai muraba'in mita 25,000, gonar kuma da ke fitar da furen Carnation da yawansu ya kai sama da miliyan 20 a kowace shekara.

To,a shirinmu na yau, za mu ziyarci wannan malamin da ke noman furanni a yankin Dounan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China