130617_Iran_Amina
|
An bayyana sakamakon babban zaben kasar Iran a daren ranar 15 ga wata, dan takara daya tak na kungiyar masu ra'ayin mazan jiya, tsohon babban wakilin kasar Iran wajen yin shawarwarin nukiliya Hassan Rouhani ya lashe zaben.
Kasashen duniya sun bayyana ra'ayoyinsu daban-daban kan wannan sakamako Ranar 15 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ba da sanarwa ta bakin kakakinsa ya taya Hassan Rouhani murnar lashen zaben. A cikin sanarwar da ya bayar, ya ce, yana mai da hankali sosai kan zaben, kuma yayi farin ciki sosai da ganin yawan masu kada kuri'u. Ban Ki-Moon ya ce, yana fatan ci gaba da hadin gwiwa da shugabanni a kasar Iran domin dukufa kan harkokin kasashen duniya da kawo zaman alheri ga jama'ar kasar. Kuma zai ci gaba da baiwa Iran kwarin gwiwa wajen taka rawa kan harkokin kasa da kasa.
Game da nasarar Hassan Rouhani ga mukamin shugaban kasar Iran, Amurka ta ce, ta mutunta burin jama'ar kasar Iran, tare kuma da nanata fatanta na warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar diplomasiyya. Kakakin fadar shugaban kasar Amurka Jay Carney ya ba da wata sanarwa a rubuce cewa, Amurka na fatan gwamnatin kasar Iran ta iya sauraran bukatun jama'arta tare kuma da samar da wani makoma mai kyau gare su. Ban da haka, sanarwar ta ce, Amurka na fatan ci gaba da tuntubar gwamnatin kasar Iran domin kawar da damuwar da kasashen duniya ke nunawa shirin nukiliya da Iran ta dauka tare kuma da neman wani shiri da ya dace wajen warware wannan matsala ta hanyar diplomasiyya.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, Isra'ila ta mai da hankali sosai kan shirin nukiliya na kasar Iran. Yana mai cewa, babban jagorar addini Ayatollah Seyyed Ali Khamenei shi ne yake tsara shirin nukiliya na Iran, amma ba shugaban kasar ba. Kuma ya yi kira ga kasashen duniya da su kara matsawa Iran lamba kan wannan batun.
Ma'aikatar yada labarai ta kasar Rasha ta ba da labari a ran 16 ga wata cewa, shugaban kasar Vladamir Putin ya bugawa Hassan Rouhani waya domin taya shi murnar lashe zabe. A cikin waya tasa, Putin ya bayyana imanin sa na cewa, bayan hawan Hassan Rouhani a matsayin shugaban kasar Iran, zai sa kaimi ga bunkasuwar Iran, kuma zai kara habaka dangantakar dake tsakanin Rasha da Iran. Ban da haka, Putin ya ce, Rasha na fatun kara hadin gwiwa da kasar Iran a dukan fannoni domin ba da tabbaci ga zaman lafiya da karko a wannan yanki har ma a dukan fadin duniya.
Wasu manazarta a kasar sun nuna cewa, hawan Hassan Rouhani a mukamin shugaban kasar Iran ba zai kawo illa ga dangantakar dake tsakanin Rasha da Iran ba, sai dai wasu masana sun nuna cewa, abin zai sassauta dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen yama, a sa'i daya kuma, zai rage dogaron da Iran ta yi dangane da Rasha, hakan zai kawo yamutsattsen hali ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Game da batun lashen zabe da Hassan Rouhani ya yi, babban wakiliyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaro Catherine Ashton ta ba da sanarwar nuna kyakkyawar fatan ga hadin kai da EU za ta yi da sabbin shugabannin kasar Iran, tare kuma da warware batun nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya tun da wuri. Kasar Birtaniya kuwa ba ta zura ido sosai kan wannan batu ba. Kafin a gabatar da sakamakon zaben, firaministan kasar Birtaniya David Cameron ya shedawa manema labaru cewa, tsarin da Iran ta bi wajen yin zabe bai kasance hakikanin hanyar demokuradiya ba.
A ganin wasu kasashe dake yankin gabas ta tsakiya wadanda suke da dankon zumunci tsakaninsu da kasar Iran sun nuna farin ciki sosai ga hawan Hassan Rouhani a matsayin shugaban kasar Iran. Wasu shugabannin sun buga masa waya ba da jimawa ba bayan aka sanar da kasancewarsa sabon shugaban kasar Iran. A cikin wayarsa, sarkin Saudiya Abdullah Bin Abdul-Aziz ya nuna fatansa na kara hadin kai da kasar Iran.
Sarkin Qatar Sheikh Hamad Bin Khalifa Al-thani da mai jiran gadon sarauta Tamim su ma sun bugawa Hassan Rouhani wayar taya murna.
Shugaban kasar Sham Bashar al-Assad kuwa ya bugawa Hassan Rouhani waya a ran 16 ga wata, a cikin wayarsa, Bashar al-Assad ya ce, kasar Sham za ta ci gaba da raya dangantakar hadin kai a dukan fannoni tsakaninta da kasar Iran, musamman ma hadin gwiwa tsakaninsu wajen tinkarar hare-haren da aka kai musu. (Amina)