in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin kide-kide da raye-raye don murnar bikin Duanwu na kasar Sin a jami'ar Legas
2013-06-09 16:20:40 cri


Ranar 12 ga watan Yuni na wannan shekara, rana ce ta wani bikin gargajiya na al'ummar kasar Sin, wato bikin Duanwu ke nan, wanda ake kiransa Dragon-Boat Festival a turance. Domin murnar wannan rana, da kuma fadakar da jama'ar Najeriya kan wannan bikin kasar Sin, an yi wani kasaitaccen bukin kade-kade da raye-raye a jami'ar Legas a ranar 7 ga wata da yamma. Yanzu ga cikakken rahoton da wakilinmu Murtala ya hada mana.

Bukin dai ya samu halartar manyan jami'ai da dama, ciki har da mataimakin karamin jakadan Sin dake Legas Mista Qiu Jian, shugabar kwalejin Confucius ta jami'ar Legas malama Jiang Lirong da dai sauransu.

A cikin jawabin da ya gabatar, mataimakin karamin jakadan Sin dake Legas Mista Qiu Jian ya bayyana farin-cikinsa game da halartar wannan gagarumin biki tare da matasan Najeriya a jami'ar Legas. Mista Qiu ya ce:

Ya ce, bukin Duanwu, buki ne mai dadadden tarihi ga al'ummar Sinawa. Ina nuna godiya ga dukkanin malaman kwalejin Confucius, saboda irin kokarin da kuke yi na ilmantar da jama'ar Najeriya kan bukukuwan gargajiya na kasar Sin. Haka kuma bari in mika godiya ga jami'ar Legas, saboda samar da wannan zarafi gare mu wajen tallata al'adun gargajiya na kasar Sin.

Masu sauraro, kidan da kuke saurara yanzu, wani shahararren kidan gargajiya ne na kasar Sin mai suna "Liang Zhu", ko kuma Butterfly Lovers a turance. Wannan buki dai ya samu halartar daliban makarantun firamare da sakandare da dama na birnin Legas, inda suka sanya tufafin gargajiya na kasar Sin masu kyan-gani, da rera wakoki da yin raye-rayen gargajiya, a kokarin bayyana fahimtarsu dangane da al'adun gargajiya na kasar ta Sin.

Har wa yau kuma, wasu daliban makarantar firamare na Legas sun karanta rubutattun wakokin gargajiya na kasar Sin a wajen bukin, abun da ya ba mu mamaki sosai.

Domin taimakawa matasan Najeriya kara fahimtar bukin gargajiya na Duanwu, malaman Confucius sun yi shiri sosai. Shugabar kwalejin Confucius ta jami'ar Legas malama Jiang Lirong ta bayyana cewa:

"Mun shiryawa matasan Najeriya abincin gargajiya a lokacin bikin Duanwu wato Zong Zi, wadanda aka shigo da su ne daga kasar Sin. Muna fatan jama'ar za su kara fahimtar wannan biki daga dukkanin fannoni. Mun kuma bukaci daliban makarantu daban-daban da su rera wakoki da yin raye-raye wadanda suka jibanci al'adun kasar Sin. Muna fatan matasan Najeriya za su so al'adun kasar Sin."

Wani dalibin jami'ar Legas mai suna Fadairo Opeyemi Yusuf yayi karatun harshen Sinanci na shekaru biyu a kwalejin Confucius, inda a wajen bukin, ya rera wata waka cikin Sinanci tare da abokiyar karatunsa. Ya bayyana cewa, bukin da aka yi yau ya kara fadakar da shi kan bukin Duanwu na al'ummar Sinawa, kuma abun da yake so yayi yanzu shi ne, dandana abincin Zong Zi.

Ga abun da ya fada:"Ban ci Zong Zi ba har yanzu. Zan ci in mun gama bikin na yau. Gaskiya ta hanyar yin karatu a kwalejin Confucius, ilmina ya karu sosai dangane da harshen Sinanci da al'adun gargajiya na kasar Sin. Ina so in je kasar Sin don gani da idona."

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Legas, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China