130601murtala
|
Ranar 1 ga watan Yuni na kowace shekara, rana ce ta yara ta duniya, wato International Children's Day a turance. A game da wannan rana, wakilinmu dake Najeriya Murtala ya ziyarci karamar hukumar Karu dake jihar Nassarawa, inda ya sadu da wata yarinya mai shekaru bakwai da haihuwa, Amina Aliyu. Ita dai wannan yarinya tana taimakon iyayenta wajen sayar da abinci domin samun kudin karatu. Duk da yake mahaifanta na fama da talauci, ba ta taba daina tunanin burinta ba na karatu don wata rana ta zama malamar jinya wato nas ba a nan gaba in ta girma.