Tun kafuwar wannan kungiya a shekarar 1963, nahiyar Afrika ta fuskanci kalubaloli sosai, duk da haka ta samu ci gaba. A halin yauzu, yaya Afrika ta samu sabon ci gaba ya zama muhimmin abu ne da shugabanni suka tattauna. A cikin wani taron manema labaru da aka yi bayan taron, shugabar kwamitin AU madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce:
"Bai kamata mu dogaro da taimako daga kasashen waje kawai kamar yadda muka saba yi a baya ba. Muna maraba da kuma karbo taimakon da za a bayar tare da nazarin yadda za mu raya manyan ababen more rayuwa da karfin kanmu, har ma da wasu ayyuka da za su karawa Afrika arziki da wadata kafin shekarar 2063."
Bisa kididdigar da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya bayar, an ce, kasashe guda goma da suka fi samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya, guda shida suna Afrika. Akwai kyakkyawar makoma ga bunkasuwar tattalin arzikin Afrika saboda ganin saurin bunkasuwarta. Duk da haka, akwai wasu matsalolin da nahiyar take fuskanta, ciki hadda cewa nahiyar ba ta samu bunkasuwa a dukan fannoni, da kuma yawan dogaro da makamashi. An sami darasi daga tarihi cewa, ana iya kyautata irin wannan tsari, muddin nahiyar ta dogaro da karfin kanta. Taimakon da kasashen yamma suka bayar ya ragu sosai, musamman ma bayan barkewar matsalar hada-hadar kudi a duniya a shekarar 2008.
Ban da haka, kasashen Afrika sun fahimci cewa, taimakon da kasashen yamma suka bayar su kan zo ne tare da sharudda masu tsanani. Abin da ya sa, shugabannin Afrika suka nanata sau da dama cewa, ya kamata, a raya nahiyar Afrika ta dogaro da karfin kanta.
Ya zuwa yanzu, ko da yake ana cikin kwanciyar hankali a wurare da dama a Afrika, amma a wasu yankuna kuwa, ana fama da rikice-rikice, kamar a yammaci, tsakiyar Afrika da kuma arewa maso gabashin Afrika. Jami'in kwamitin kula da harkokin zaman lafiya da tsaro na AU Ramtane Lamamra ya shedawa wakilinmu cewa:
"Muna fatan kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa tsakaninmu da kasar Sin, kuma muna da kyakkyawar fatan hadin kai da kasar Sin kan batun tsaro. A ganina, Sin za ta ba da taimako sosai ga aikin shimfida zaman lafiya a nahiyar. Ban da haka, Sin za ta iya ba da taimako gare mu wajen horar da sojojinmu tare kuma da kara mana makamai."
Dadin dadawa, Ramtane Lamamra ya ce, an zartas da wani muhimmin kuduri wanda ya nemi a kafa wata runduna mai kula da halin ko ta kwana dake karkashin shugabancin AU, ta yadda za a iya warware rikicin ba zato ba tsammani yadda ya kamata.
Shugabannin kasa da kasa sun halarci taron, ciki hadda shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ministan harkokin waje na Amurka John Forbes Kerry, shugabar kasar Brazil Madam Dilma Rousseff da sauransu. Wakilin musamma na shugaban kasar Sin kuma mataimakin firaministan kasar Wang Yang kuwa, a matsayin wakilin nahiyar Asiya ya karanta wasikar nuna kyakkyawar fata da shugaban kasar Xi Jinping ya rubuta. (Amina)