Gandun gona na kasar Sin ya taimakawa Nijeriya wajen samar da hatsi da kanta
|
Kwanan baya ne, aka kawo karshen lokacin rani a yammacin Afrika, inda aka yi girba mai dinbin yawa a cikin wata gonar 'yan kasar Sin dake jihar Kebbi. Hatsi da aka girba daga wannan gona ya zama wani muhimmin mataki wajen taimakawa kasar Nijeriya dangane da canja hanyar da take bi a fannin sha'anin noma. Sinawa a wurin na kokarin taka rawa ta yadda za su taimakawa kasar Nijeriya wajen samar da hatsi da karfin kanta. Wannan gandun gona na nan ne a yankin dake kan iyakar jihar Kebbi da ta Nijer a arewa maso yammacin kasar Nijeriya. Yanzu, ana kokarin girbin hatsi.