in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar farko ta shugaban kasar Sin Xi Jinping ta jawo hankalin kasa da kasa sosai
2013-04-01 15:45:32 cri






A ranar 31 ga watan Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dawo birnin Beijing na kasar Sin, bayan ya kammala ziyararsa a kasashen Rasha, Tanzania, Afirka ta Kudu da kuma Jamhuriyyar Congo tare da halartar taro karo na biyar na shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS da aka yi a kasar Afirka ta Kudu. Wannan ne karo na farko da Xi Jinping ya kai ziyara a kasashen waje bayan da ya hau kujerar shugabancin kasar Sin, dalilin da ya sanya wannan ziyara ta jawo hankalin kasa da kasa sosai.

Game da ziyarar shugaba Xi Jinping a wannan karo, shugaban cibiyar nazarin batutuwan duniya ta kasar Sin, Qu Xing ya nuna cewa, ziyarar ta mai da hankali kan dangantakar dake tsakanin manyan kasashe, kasashen dake makwabtaka, kasashe masu tasowa, da kuma bayyana sabbin manufofin diplomasiyya da sabbin shugabannin kasar Sin za su bi. Qu Xing ya ce,"Kasar Rasha a matsayin kasar farko da shugaba Xi ya kai wa ziyara ta bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninta da manyan kasashe, da tsaro a kan iyakar kasa da kasa, kana ta nuna cewa, dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Rasha dangantaka mafi muhimmanci ga kasar Sin. Ziyararsa a kasashen Afirka ta bayyana cewa, Sin na sa lura sosai kan dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa, musamman ma a tsakaninta da kasashen Afirka. Shugaba Xi ya halarci taron kungiyar BRICS, da nuna goyon baya ga batutuwan da aka tattauna da kuma yaba muhimmiyar rawar da tsarin kungiyar BRICS yake taka, wannan ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin ya mai da hankali kan dangantakar dake tsakanin kasashen duniya."

Kasar Rasha kasar farko ce da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a wannan karo, inda bangarorin biyu suka zurfafa fahimtar juna da goyon baya ga juna bisa manyan tsare-tsare. Shekaru 10 masu zuwa za su kasance muhimmin lokaci ga kasashen biyu wajen samun ci gaba, ta yadda hadin gwiwarsu zai taimaka musu wajen cimma wannan buri.

Ziyarar shugaba Xi a kasashen Afirka ita ma ta zama ziyara mai muhimmanci ga kasar Sin. Yayin da shugaba Xi yake ziyara a nahiyar Afirka, an daddale yarjeniyoyi fiye da 40 na hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ciki har da wasu manyan ayyukan raya kasa da inganta rayuwar jama'ar kasashen Afirka. Kana shugaba Xi ya sanar da wasu matakan fahimtar juna da yin mu'amala a tsakanin jama'ar Sin da ta kasashen Afirka. Tsohon wakilin Sin mai kula da harkokin Afirka kuma tsohon jakadan Sin dake Afirka ta Kudu Liu Guijin ya jaddada cewa,"A cikin jawabin shugaba Xi, ya jaddada cewa, ana dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin tattalin arizki da cinikayya tare da kara yin mu'amalar al'adu a tsakaninsu. Yayin da ake inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, ya kamata a kara inganta hadin gwiwa a fannin al'adu. Domin idan aka zurfafa zumunci a tsakanin jama'a, to ko shakka babu za a zurfafa tushen dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka."

Ban da wannan, shugaba Xi Jinping ya halarci taron shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS karo na biyar da aka yi a Durban dake kasar Afirka ta Kudu. Game da wannan, Liu Guijin ya bayyana cewa,"Kasar Sin ita ce muhimmiyar membar kungiyar BRICS, yawan kudin da aka sarrafa daga dukiyar kasar wato GDP ya zama matsayin farko a cikin kungiyar. Amma ita ce wata membar kungiyar da matsayinta ya yi daidai da sauran membobin kungiyar. Kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran kasashe membobin kungiyar wajen kara yin hadin gwiwa cikin adalci da samun moriyar juna da kuma samun bunkasuwa mai dorewa bisa tsarin kungiyar BRICS da kuma dandalin tattaunawa a tsakaninta da kasashen Afirka." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China