in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaba Xi Jinping tana da ma'ana sosai, in ji ministan kasar Sin
2013-04-01 15:45:02 cri






Tun daga ranar 22 zuwa ranar Asabar 30 ga watan na Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da ziyara a kasashen Rasha, da Tanzaniya, da Afirka ta Kudu, da Jamhuriyar Congo, ya kuma halarci taron shugabannin kasashen BRICS karo na 5.

Bayan kammala wannan ziyara, ministan harkokin wajen kasar Sin, Mista Wang Yi, ya bayyana sakamakon da aka samu daga ziyarar.

A cewar Mista Wang Yi, wannan ziyara ta kasance irinta na farko da sabbin shugabannin kasar Sin suka yi bayan da suka dare karagar mulki, haka kuma ta zama mabudin ayyuka a fannin diplomasiyya, tare da nuna manufar kasar wajen hulda da kasashen waje, wato batun girmama 'yancin kai, da rungumar zaman lafiya. Ziyarar da shugaba Xi Jinping ya yi ta hada da bukukuwa 66, da ganawa da shugabanni 32 na kasashe daban daban, da gudanar da jawabai fiye da karo 20, inda ya bayyana manufofin kasar Sin dalla-dalla a fannoni daban daban. Haka zalika ya halarci bukukuwa fiye da 10 masu alaka da al'adu da cudanyar jama'a.

A ganin minista Wang, ziyarar shugaba Xi Jinping ta haifar da sakamako a wasu fannoni da suka hada da na farko, karfafa zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasar Rasha, Ganin yadda shugaba Xi ya mai da kasar ta Rasha kasa ta farko da ya kaiwa ziyara bayan da ya hau kujerar mulki, hakan ya dace da abin da aka saba da shi tsakanin kasashen 2 tun a shekarun baya.

Bugu da kari kuma, hakan ya shaida muhimmancin huldar abota dake tsakanin kasashen 2, wadda ta shafi manyan tsare-tsarensu. A wannan karo, shugabannin Sin da na Rasha sun yi tsawon sa'o'i 8 suna tattunawa, ta yadda suka cimma ra'ayi daya, kan yadda za a kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen 2, matakin da kuma zai zama jagora ga aikin raya huldar dake tsakaninsu. Haka zalika, ziyarar shugaba Xi ta dada karfafa imanin dake tsakanin bangarorin Sin da Rasha, ganin yadda ma'aikatar tsaron kasar Rasha da cibiyar ba da jagoranci ga sojojin kasar suka bude kofa a karon farko, don karbar ziyarar wani shugaban waje.

Ban da haka, ziyarar ta zurfafa hadin kan kasashen 2 bisa la'akari da yadda aka sa hannu kan takardu 32, wadanda suka shafi ayyukan hadin gwiwa daban daban.

Na biyu daga sakamakon ziyarar ta shugaba Xi,shi ne tabbatar da zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Duba da yadda shugaban ya ziyarci nahiyar a karon farko, bayan zamowarsa shugaban kasar Sin, hakan ya nuna cewa, kasar Sin ta darajanta zumuncin da ya dade tsakaninta da Afirka. A jawabin da ya yi a kasar Tanzaniya, shugaba Xi Jinping ya yi wasu kalamai dake bayyana manufar kasar Sin wajen hulda da kasashen Afirka, wato gudanar da gaskiya, da daukar matakai na hakika, da karfafa zumunci, da nuna aminci.

Ta wannan ziyara, an karfafa aniyar Sin da Afirka don gane da hadin gwiwarsu. Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, suna matukar bukatar ganin Sin ta inganta hadin kai tare da nahiyar, kana sun karyata zantuka marasa ma'ana dake nuna kasar Sin, a matsayin wadda ke yin sabon salon mulkin mallaka a Afirka.

A ganinsu, bangarorin biyu suna hadin kai, don moriyar juna, da samun nasara tare, matakin da ya samu karbuwa sosai daga jama'ar nahiyar.

Yayin wanna ziyara ta shugaba Xi, kasar Sin ta rattaba hannu tare da kasashen Afirka kan yarjeniyoyi fiye da 40, ciki hadda wasu manyan ayyukan da suka shafi batun kyautata zaman rayuwar jama'ar ta Afirka. Bugu da kari kuma, shugaba Xi ya sanar da jerin matakan da Sin za ta dauka don mara wa Afirka baya, ciki hadda kara karfin tallafi gareta, da hadin kai ta fuskar zuba jari da hada-hadar kudi, da horar da kwararrun da ke aiki a fannin fasahohi masu alaka da sana'o'i da dai sauransu.

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta cika dukkan wadannan alkawura ba tare da gindaya wani sharadi a siyasance ba, a kokarin tallafa wa kasashen na Afirka, wajen yada fifikonsu a fannin albarkatun ma'adinai, domin neman samun dauwamammen ci gaba bisa karfin kansu.

Sakamako na uku da aka samu a wannan ziyara shi ne, tattara karfin kasuwanni masu saurin ci gaba, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar kasashen BRICS.

A yayin ganawa a tsakanin shugabannin kasashen BRICS, shugaba Xi Jinping, ya bayyana ra'ayin kasar Sin kan fannonin da ya kamata kasashen BRICS su hada kansu, da kuma ka'idojin hadin gwiwar.

Haka nan ya bayar da shawara kan yadda za a raya dangantakar abokantaka tsakanin kasa da kasa don ci gaba, da yadda za a daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, gami da yadda za a tsara ajandar neman samun ci gaba ta kasa da kasa, tare da sa ran ganin kasashen BRICS, sun yi kokarin kafa babbar kasuwar cinikayya da zuba jari bai daya, da kyautata cudanya ta fuskar kudi, da inganta hadin gwiwarsu wajen raya muhimman ayyukan more rayuwar jama'a daga dukkan fannoni, kana da kara mu'amala a tsakanin jama'a.

Dukkanin wadannan ra'ayoyi suna nuni ga hadin gwiwar kasashen BRICS a nan gaba, wadanda suka samu yabo da amincewa daga bangarori daban daban.

A yayin taron dai an daddale yarjeniyoyin hadin gwiwa da dama, da kuma tsai da kudurin kafa bankin raya kasashen BRICS, da dai sauransu. Kana an samu ra'ayin bai daya, kan yadda za a fuskanci lamuran duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankalin kasa da kasa, da yadda za a yi kwaskwarima ga tsarin kudi na duniya da dai sauransu. Duk wadannan matakai sun sheda kokarin da kasashen BRICS ke yi wajen hadin kansu don samun nasara tare.

A karshe dai, minista Wang Yi ya furta cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping ya samu kyawawan sakamako, wadda zai ba da taimako wajen kiyaye zaman karko a yankin da kasar Sin ke ciki, da aza harsashi mai inganci ga harkokin diplomasiyyar kasar Sin, gami da kara azama kan samun demokiradiyya, yayin da ake raya dangantaka a tsakanin kasa da kasa.( Bello Wang / Kande)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China