in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne kasar Sin da kasashen Afrika su yi kokarin raya dangantakarsu, in ji kwararru
2013-04-01 15:45:02 cri






A ranar 29 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bar kasar Afrika ta Kudu kuma ya yi tattaki zuwa Kongo(Brazzaville) zangon karshe cikin ziyararsa ta wannan karo. Daga kasar Tanzaniya da ke yankin gabashin nahiyar Afrika, zuwa Afrika ta Kudu da ke kudancin nahiyar, har zuwa kasar Kongo(Brazzaville) dake yankin yammacin nahiyar Afrika, ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a wadannan kasashen Afrika ta nuna cewa, kasashen Afrika na da matsayin musamman cikin manufar diplomasiyya ta kasar Sin. Yanzu, ga abokin aikina Bako da karin bayani.

Kwanan baya, tsohon manzon musamman na gwamnatin kasar Sin game da harkokin kasashen Afrika Liu Guijin ya bayyana cewa, ziyarar shugaban kasar Sin a wannan karo na da muhimmiyar ma'ana. Yadda shugaban kasar Sin ya kai ziyararsa ta farko a Afrika ta nuna wa jama'ar kasashen Afrika cewa, sabbin shugabannin kasar Sin za su ci gaba da mai da muhimmanci kan nahiyar da kuma dangantakar bangarorin biyu. Kazalika kuma, ya nuna cewa, ginshikin manufar diplomasiyyar kasar Sin shi ne, raya hadin gwiwa tsakaninta da kasashe masu tasowa. Haka kuma, a cikin sabon yanayin da ake ciki yanzu, shugabannin kasar Sin da kasashen Afrika za su mai da hankali kan sabbin matsalolin da suke bullowa game da dangantakar da ke tsakaninsu a yayin da suke tattauna kara inganta hadin gwiwa a tsakaninsu.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya samu habaka cikin gaggawa, amma a sa'i daya kuma, kafofin yada labaru na wasu kasashen yammacin duniya sun ikirarin cewa, wai kasar Sin tana kwace albarkatun ma'adinai a kasashen Afrika, wato Sin tana gudanar da wani sabon nau'in mulkin mallaka a kasashen Afrika. Ban da wannan kuma, yadda kafofin yada labaru na wurin sun kan rura wuta kan kasar Sin da kasashen Afrika su kan samu rikici sakamakon masana'antunsu da yadda wasu masana'antun Sin suka keta dokokin kasar da suke ciki. Game da wannan, shugaban cibiyar nazarin batun kasa da kasa ta kasar Sin Qu Xing ya bayyana cewa, a sabon yanayin da ake ciki yanzu, kamata ta yi kasar Sin da kasashen Afrika su yi la'akari da sabbin matsalolin da suke bullowa cikin dangantakar da ke tsakaninsu, tare da gano bakin zaren warware su. Ya ce, "A bangaren kasashen Afrika, da ma, akwai shugabannin kasashen Afrika da ke sada zumunta da fahimtar kasar Sin sosai a lokacin da suke kokarin samun 'yancin kai, amma a halin da ake ciki yanzu, akasarin shugabannin kasashen Afrika sun yi karatu a kasashen yammacin duniya, don haka, tunaninsu da fahimtarsu game da kasar Sin na samun babban sauyi. Haka kuma, dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta canja daga samar da gudummawa kawai ga kasashen Afrika zuwa samun moriyar juna sosai a yanzu, abin da wasu jama'ar kasashen Afrika ba su saba sosai ba, ke nan kamata ya yi a yi nazari sosai game da wannan matsala, don lalubo hanyoyin da za a bi don warware matsala."

Haka kuma, Qu Xing ya bayyana cewa, kasashen Afrika na kan wani muhimmin matsayi cikin manufar diplomasiyya ta kasar Sin, kuma sabuwar gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga sada zumunta da kasashen Afrika. Ta bangaren kasar Sin, don raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afrika, da kuma warware matsaloli a tsakaninsu, kamata ya yi gwamnatin Sin da masana'antun Sin da suka saka jari a kasashen Afrika su yi kokari tare. Ya ce, "Yayin da masana'antun Sin suke inganta hadin gwiwar tattalin arziki da kasashen Afrika, kamata ya yi su yi la'akari da batun samun moriyar juna, da kara kawo alheri ga al'ummar wurin. Haka kuma, ya zama dole a inganta harkokin diplomasiyyar jama'a, sakamakon yadda akasarin kwararrun Afrika suka yi karatu ne a kasashen yammacin duniya, don haka, su kan samu rashin fahimta kan samun daidaito wajen raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, sannan kuma, wasu kafofin yada labaru sun kan rura wuta tare da murde gaskiya kan wasu batutuwa.

A karkashin sabon yanayin da ake ciki, kamata ya yi a ci gaba da rike dankon zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, sabo da akwai makoma mai haske wajen raya dangantakar bangarorin biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China