in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin taimakawa kasashen Afirka wajen kara fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin
2013-04-01 15:45:02 cri






Yanzu haka shugaban kasar Sin Xi Jinping yana ci gaba da ziyararsa a nahiyar Afirka. Yadda sabon shugaban ya je nahiyar Afirka a ziyararsa ta farko, ya sheda cewa kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Bari mu saurari wani bayani da Bello Wang ya hada mana, dangane da kokarin da kasar Sin take yi don raya harkar cinikayya a tsakanin Sin da Afirka.

A shekarun baya, yayin da hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin ke kara saurin bunkasa tare da samun ingantuwa, bangarorin 2 suka cimma manyan nasarori kan hadin kansu a fannin tattalin arziki da cinikayya. Alkaluma sun sheda cewa, yawan kudin cinikayyar da kasashen Afirka suka yi da kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 200 a shekarar 2012. Sai dai ya kasance da wasu matsalolin da suka shafi tsarin cinikayyar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, wadanda ke bukatar a daidaita su. Ga misali, yawancin kayayyakin da kasashen Afirka ke fitar da su zuwa kasar Sin albarkatu ko kuma danyun kayayyaki ne, kana a cikinsu kayayyakin dake tattare da karin daraja ba yawa. Don daidaita wadannan matsaloli ta yadda za a zama dacewa da manufar da kasar Sin ke bi wajen hadin kai da sauran kasashe wato tabbatar da moriyar juna, kasar Sin ta dauki wasu matakai don taimakawa kasashen Afirka kara fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin.

Daya daga cikin matakan, shi ne ba da tallafi ga kasashen Afirka a fannin karbar haraji kan kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasar Sin. Dangane da matakin, Chen Demin, tsohon ministan cinikayya na kasar Sin, ya bayyana cewa,

'Kasar Sin na kara bude kofarta ga kasashen Afirka, inda ta yi amfani da manufarta ta yafe haraji kan kayayyakin da wasu kasashen Afirka mafi talauci ke fitarwa don amfanawa kasashe 31 dake nahiyar Afirka. A nan gaba, galibin kayayyakin da wasu kasashe marasa ci gaba ke fitar zuwa kasar Sin ba za a karbi haraji kansu ba.'

An soma wannan manufar ba da tallafi ga kasashen Afirka marasa ci gaba a shekarar 2005. Zuwa watan Janairu na shekarar 2012, manufar ta shafi kashi 60% na kayayyakin da wasu kasashen Afirka suke fitarwa, sai dai a nan gaba za a habaka jimillar zuwa kashi 95%. Bayan da aka fara daukar wannan manufa, an riga an samu nasarar kara yawan kayayyakin da kasashen Afirka suke fitarwa zuwa kasar Sin.

Wani mataki na daban da gwamnatin kasar Sin ta dauka don kara azama ga aikin fito da kaya ga kasar Sin da kasashen Afirka suke yi, shi ne gudanar da bukukuwan baje kolin kayayyakin kirar kasashen Afirka. Zuwa yanzu an riga an shirya bukukuwan irin haka karo 4. Sa'an nan dalilin da ya sa aka shirya bukukuwan shi ne domin a nuna kayayyakin kasashen Afirka, da taimakawa kamfanonin kasashen shiga cikin kasuwannin kasar Sin, da kara kayayyakin da kasar Sin ke shigo da su daga kasashen Afirka, don tabbatar da daidaituwa kan cinikayyar da ake yi tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Malama Refina Fatima 'yar kasar Tanzaniya ce, wadda ta halarci bikin baje kolin kayayyakin kasashen Afirka karo na 4 da ya gudana a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin a watan Nuwamban bara, inta ta yi bajen wani kaya mai yanayin musamman na Afirka, wato kayan sassaken itace. Malama Refina ta ce,

"Wannan kaya na samun karbuwa sosai a nan kasar Sin. Sassaken itace shi ne kayan da Sinawa suka fi son saya a lokacin da suka tafi kasashen Afirka, amma ba dukkan Sinawa ke da damar zuwa Afirka ba, don haka bikin baje koli kamar haka zai sa karin yawan Sinawa sanin kayayyakinmu."

Ban da haka kuma, kafa wata cibiyar nune-nunen kayayyakin kasashen Afirka shi ma ya kasance cikin matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka don taimakawa kasashen Afirka kara fitar da kaya zuwa kasar Sin.

Wannan cibiyar an kafa ta a babbar kasuwar cinikayyar kasa da kasa dake birnin Yiwu na gabashin kasar Sin, wadda fadinta ya kai mita 5000. A watan Mayu na shekarar 2011 ne an fara bude cibiyar, inda ake baje kolin kayayyaki iri-iri fiye da 2000 wadanda aka kera su a wasu kasashen Afirka 27 da suka hada da Kenya, Tanzaniya, Zimbabwe, Tunisia, Masar, Afirka ta Kudu, Ghana, Senegal, Benin, Niger, Habasha, da dai makamantansu. Don kara janyo hankalin 'yan kasuwan kasashen Afirka su kafa shaguna cikin cibiyar, an samar da jerin manufofin tallafi, kamar yadda Zhu Xinping, mataimakin darektan cibiyar ya bayyana,

'Da farko, mun ba da gatanci a fannin kudin hayan shaguna. Ko kwabo daya ba za mu karba ba daga 'yan kasuwan kasashen Afirka kan yin amfani da shagunanmu, haka kuma ba sa bukatar biyan kudin kula da shaguna wato management, da kudin AC da dai makamantansu. Na biyu, mu kan sanya su nuna kayayyakinsu a wurare daban daban na kasar Sin a ko wace shekara, inda mu kan ba su tallafi a fannin kudin da suke bukata. Na uku, mu kan ba su taimako wajen ayyukan neman visa, da samar da takardar gayyata. Na hudu, muna musu hidima a fannonin hada-hadar kudi, sufurin kaya, da aikin kwastam, da dai sauransu.'(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China