in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na gano darajata a kamfanin Huawei——kamfanin kasar Sin a idon wata ma'aikaciyar Nijeriya
2013-04-01 15:45:02 cri






A yayin da Sin da kasashen Afirka ke kara hulda da juna a fannin cinikayya cikin 'yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin suna ta kara gudanar da harkokinsu a kasashen Afirka, wadanda kuma ke ta shigar da 'yan Afirka a cikin ma'aikatansu. Ma'aikata 'yan Afirka suna ba da muhimmin taimako ga bunkasuwar kamfanonin kasar Sin, a yayin da kuma suke ganin canji a rayuwarsu.

"Na kama aiki da kamfanin Huawei a shekarar 2005, yanzu shekaru sama da 7 ke nan, kuma ina kula da albarkatun ma'aikata a cikin kamfanin." Huawei wani kamfani ne na kasar Sin da ke gudanar da harkokin sadarwa a kasashe daban daban, kuma Josephine tana daya daga cikin ma'aikata 'yan Afirka sama da 700 a reshen kamfanin Huawei dake yammacin Afirka. Tun daga lokacin da ta kama aiki da kamfanin Huawei a shekarar 2005, a yanzu haka tana kujerar manajan kula da albarkatun jama'a na kamfanin a yankin Abuja na kasar Nijeriya. A yayin da aka tabo magana kan dalilin da ya sa ta zabi wannan kamfanin kasar Sin, Josephine ta ce, dalilinta ya zo daya da na dimbin ma'aikatan Nijeriya, wato samun damar karo ilmi, inda take cewa,"Dalilin da ya sa na zabi kamfanin kasar Sin shi ne ina son kalubale, inda zan samu wayewar kai. Ban taba zuwa kasar Sin ba, amma ina ganin zan iya karo ilmi kan wannan kasa a yayin aiki cikin kamfanin kasar."

To amma, bayan da ta kama aiki a cikin kamfanin, sai ta gano cewa, aikin ba shi da sauki kamar yadda ta yi zato. Josephine tana mai cewa,

"kafin na fara aiki a kamfanin, ina iya cewa, ni mace ce mai alfahari sosai, amma da na zo kamfanin, sai na tarar da cewa, dole ne ka ajiye abin da ka sani game da kanka, kuma ka yi kokarin karo sabon ilmi, a hakika, abin da ya kamata a koya suna da yawa."

Dole ne mutum ya zamo kwararre domin ya cancanci aiki a kamfanin sadarwa. Domin ma'aikatansa su samu fasahohin da ake bukata, a shekarar 2006, kamfanin Huawei ya kafa wata babbar cibiyar horaswa a birnin Abuja, inda yake horar da ma'aikatansa fasahohin zamani. Ban da haka, ya kuma tura wasu ma'aikatansa 'yan Afirka zuwa kasar Sin, don a zurfafa ilminsu ta fannin nazari da gwaje-gwaje. A game da wannan, Gao Xiang, shugaban sashen kula da harkokin fasaha na kamfanin Huawei a yammacin Afirka ya bayyana cewa,"kamfaninmu na kokarin daukar ma'aikata 'yan Afirka. Daga cikin ma'aikatanmu 1200, akwai 700 da suka kasance 'yan Afirka. A cikin shekaru shida zuwa bakwai da suka gabata, ma'aikatanmu 'yan Afirka sun gudanar da kashi 99% na aikin gina tashoshinmu na sadarwa."

Baya ga ci gaban harkokinsa da ya samu, kamfanin Huawei yana kuma samar da dimbin guraben aiki a Nijeriya, tare kuma da samar da kwararru a fannin sadarwa. A kamfanin, ma'aikata 'yan Nijeriya sun gano darajarsu tare kuma da tabbatar da darajar, kamar yadda Josephine ta bayyana,"Huawei kamfani ne da zai taimake ka ka zamo mai alfahari. Da na fito daga nan, kullum na kan ce ma aminaina, ba don kudi kawai nake aiki a nan ba, ina yi ne domin yadda nake iya tabbatar da darajata ne."

Josephine wadda a yanzu haka ta yi shekaru 7 tana aiki a kamfanin Huawei, ta ce, a cikin shekarun 7 da suka gabata, babban sauyin da ya faru gare ta shi ne yadda take tunani kan abubuwa. Ta ce tana son irin alfaharin da kamfanin kasar Sin yake kawo mata, kuma tana fatan za ta iya ci gaba da aiki da kuma karatu a kamfanin. Josephine ta yi murmushi ta ce, mai yiwu nan gaba za ta zama shugaba ta kamfanin, ta ce, "maganar makomata, mai yiwuwa zan iya zama shugaban Huawei. Yanzu haka ina kula da harkokin albarkatun jama'a, tana yiwuwa nan gaba zan samu damar zama shugaba, abin ya danganta ne ga irin taimakon da na bayar ga kamfanin. Ina kuma shirin koyon Sinanci, amma yana da dan wuya, duk da haka yarana suna koya. Ban da haka, ina fatan zan iya zurfafa ilmina, ba zan bar aiki a nan ba."

A hakika, kamfanin Huawei daya ne kawai daga cikin kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da harkokinsu a Afirka, kuma Josephine na daya daga cikin dubun dubatar ma'aikatansu 'yan Afirka. Domin buri daya ne ke hada kansu, wato kokarinsu na bunkasa harkokin kamfanonin kasar Sin a Afirka tare da tabbatar da ci gaban zaman al'ummar wurin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China