in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za ci gaba da kokarin kyautata huldar dake tsakanin Sin da Afirka, in ji shugaban kasar Sin
2013-03-28 21:09:15 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi taron karin kumallo tare da shugabannin wasu kasashen Afirka, a ranar Alhamis 28 ga wata, a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, inda shugabannin suka yi musayar ra'ayi kan huldar dake tsakanin Sin da Afirka, da yanayin da nahiyar Afirka ke ciki.

A wajen taron, shugabannin kasashen Afirka sun yaba a kan zumuncin da ya dade tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. A cewar shugabannin, zancen wai kasar Sin tana masu mulkin mallaka a nahiyar ba taso ba kuma ba ya da tushe. A ganinsu a zahiri ma, kasashen Afirka ne suke son koyon fasahohin kasar Sin wajen neman ci gaba, da kokarin karfafa hadin kai tare da kasar Sin, gami da fatan ganin kasar Sin ta ci gaba da rufa ma kasashen Afirka baya a wuraren da suka shafi huldar kasa da kasa. Don haka suka yi alkawarin cewa, kasashensu ma za su ci gaba da goyon bayan kasar Sin.

Bayan da ya saurari jawaban shugabannin kasashen Afirka, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, a wannan lokacin da ake samun sauye-sauyen yanayin duniya, huldar dake tsakanin Sin da Afirka na fuskantar dama, tare da kalubale. Sai dai a duk wani yanayin da ake ciki, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa kan manufarta ta kulla zumunci tare da kasashen Afirka, kuma za ta ci gaba da zama aminiya ga kasashen Afirka da sahihiyar abota, sa'an nan kuma za ta yi kokarin samar da gudummowa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China