in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu ma'ana wajen ruruta maganar amfanin tashar Bagamoyo a fannin aikin soja, in ji hafsan kasar Sin
2013-03-28 20:27:06 cri
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin kanar Yang Yujun ya bayyana a wani taron manema labaru da aka yi a ranar Alhamis 28 ga wata cewa, kokarin da ake yi wajen ruruta maganar amfanin tashar Bagamoyo da ke kasar Tanzaniya a fannin aikin soja ba shi da ma'ana.

Kanar Yang ya bayaa cewa, aikin habaka tashar jiragen ruwa ta Bagamoyo ya kasance daya daga cikin ayyukan hadin gwiwa da kasashen Sin da Tanzaniya suke aiwatarwa a fannin cinikayya. Aikin, da a cewar kanar Yang, ya dace da moriyar bai daya ta jama'ar kasashen 2, tare da amfanawa tattalin arzikin wurin da za a gudanar da aikin.

Kanar Yang ya ce, a kan alakanta ayyukan gina tashoshin teku da kamfanonin kasar Sin suka halarta da sojojin kasar Sin, inda ake kokarin ruruta ainihin ma'anarsu da cewa tashoshin na da alaka da aikin soja, abin da a cewar sa ba shi da ma'ana ko kadan. Yana mai tabbatar da cewa, a hakika, ka'idojin kasa da kasa sun kayyade cewa, jiragen ruwan yaki na kowace kasa za su iya yada zango a ko wace tashar ruwa ba tare da lura da cewa wai ta mallake ta ko kuma kula da ita ba, illa dai kawai suna bukatar izini daga kasar dake da tashar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China