in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gabatar da jawabi, a ganawarsa da shugabannin kasashen BRICS
2013-03-28 17:58:29 cri






An yi ganawa karo na biyar na shugabannin kasashen BRICS a birnin Durban na kasar Afrika ta kudu a ran 27 ga wannan wata. Inda aka kulla yarjeniyoyi, da dama tare da cimma matsaya daya don gane da kafa Bankin raya kasashen BRICS da asusun kudaden musaya na kungiyar.

Wannan ne dai karo na farko da aka gudanar da ganawa tsakanin shugabannin BRIKS a Afrika, shugabannin kasashen BRICS biyar, ciki hadda shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, da shugaban Vladimir Vladimirovich Putin na Rasha da kuma shugaban kasar Brazil Dilma Rousseff da kuma firaministan kasar Indiya Manmohan Singh sun halarci ganawar da aka yi a wannan rana.

Shugabannin sun dai tattauna bisa jigon "Raya dangantakar abokantaka dangane da samun bunkasuwa, da gaggauta tsarin dunkulewa, da raya masana'antu". Inda shugaba Xi kuma ya ba da jawabinsa mai teken "Hadin gwiwa domin samun bunkasuwa tare", inda cikin jawabin ya ce:

"Sinawa kan ce, babu nisa tsakanin masu buri iri daya. Kasashen BRICS dake da asali daga nahiyoyi daban-daban, sun hada hai da juna domin cimma burin kulla dangantakar sada zumunci da samun ci gaba juna sannan burinsu daya ne su raya dangantakar kasa da kasa bisa tsari na dimokuradiyya, tare da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar Bil Adam gaba.

Ban da haka, muna daukar nauyi bai daya, na samar da zaman lafiya, da samun bunkasuwa, da sa kaimi ga hadin gwiwa, da kuma samun moriyar juna."

Game da jigon wannan taron, Mr Xi ya nuna cewa, ya kamata, kasashen BRICS su yi iyakacin kokarinsu, wajen sa kaimi ga raya dangantakar kasa da kasa, domin samun bunkasuwa da wadata tare. Ya ce:

"Jigo a wannan karo shi ne 'kafa dangantakar hadin gwiwa, dangane da samun bunkasuwa, da gagguta tsarin dunkulewa da raya masana'antu', ba ma kawai domin burin dake tsakanin kasashen na BRICS ba, har ma ya zama muhimmiyar akida, ta yin hadin gwiwa tsakanin kasashen na BRICS da kuma kasashen Afrika. Ya kamata, mu yi amfani da irin wannan dangantaka domin hada kan kasashen BRICS, da samun bunkasuwa yadda ya kamata a fannonin tattalin arziki da ciniki, da hada-hadar kudi, da manyan ababen more rayuwa da cudanya da juna, domin cimma burin kafa wata kasuwar bai daya, da inganta mu'ammala da juna a dukkanin fannoni, da zirga-zirga kan hanyoyi daban-daban tsakaninsu, da kuma gudanarda cudanya yadda ya kamata."

Wannan karo farko ne da aka yi ganawar shugabannin kasashen BRICS a nahiyar Afrika, saboda haka, ana mai da hankali sosai kan batutuwan Afrika. Mr Xi ya bayyana cewa:

"Ya kamata, mu goyi bayan nahiyar Afrika a kokarinta na samu bunkasuwa, da ingiza tsarin dunkulewa da raya masana'antu, sannan a sa kaimi ga tattalin arzikinta domin ya zama abin da a zo a gani a bunsuwar tattalin arzikin duniya."

Dadin dadawa, a cikin jawabinsa, Mr Xi ya yi nuni da cewa, ya kamata, kasashen BRICS su kara amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa dankon zumunci dake tsakanin jama'arsu, sannan su yi kokarin raya masana'antu, da harkokin sadarwa, da birane da kuma aikin gona na zamani, sannan kuma su kara hadin gwiwa da daidaita matsayin juna bisa tsare-tsaren MDD, G20, hukumomin tattalin arziki da hada-hadar kudi na kasa da kasa. Bugu da kari za su yi kokarin tabbatar da kafa bankin raya kasashen BRICS, da asusun kudaden musayar waje, tare kuma da zurfafa hadin kai a fannoni daban-daban tsakaninsu.

Yayin da aka tabo batun samun bunkasuwar kasar Sin nan gaba, Mr Xi ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da mai da batun samun ci gaba a fannoni daban-daban a gaban kome, ciki hadda tattalin arziki, da siyasa, da al'adu, da zaman rayuwar al'umma, da muhalli. Ya kuma jaddada cewa:

"Sin za ta nace ga matsayin bude kofarta ga kasashen waje, da kawo moriyar juna. Haka nan Sin za ta yi hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da fasaha da kasashe daban-daban bisa adalci da daidaito. Bugu da kari za ta kara zurfafa hadin kai tsakaninta da kasashen BRICS a nan gaba, da kokarin amfanawa jama'ar dukkanin bangarorin, ta kuma ba da taimako ga tabbatar da zaman lafiya, da ci gaban a duniya."

Su ma sauran shugabannin kasashen BRICS sun ba da jawabinsu, kuma an ba da sanarwar Durban, tare da sanar da shirya ganawa ta gaba a shekarar 2014 a kasar Brazil. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China