in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na biyar a Durban
2013-03-28 10:06:35 cri

Ran 27 ga wata, shugabannin kasashen BRICS sun yi ganawa karo na biyar a birnin Durban, kasar Afirka ta Kudu.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, shugaban kasar Rasha Putin, da kuma firaministan kasar India Manmohan Singh sun halarci taron ganawar.

Yayin taron, shugabannin biyar sun ba da jawabai game da taken ganawar tasu wajen 'bunkasa dangantakar neman ci gaba tare da kuma raya ayyukan masana'antu.

Shugaba Xi Jinping ya yi jawabi mai taken 'hadin gwiwa wajen neman ci gaba tare,' inda ya jadadda cewa, ya kamata kasashen BRICS su tsaya tsayin daka wajen kiyaye adalci tsakanin kasa da kasa, kare zaman lafiya da karko a fadin duniya, gami da dukufa wajen inganta gina dangantakar abokantaka tsakanin kasa da kasa, da kuma karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu don cimma moriyar juna.

Ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa tare da sauran kasashen BRICS, ta yadda za a iya gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin kasashen BRICS, samun karin kyakyawan sakamakon hadin gwiwa don moriyar al'ummomin kasa da kasa da kuma ba da karin gudumawa ga zaman lafiya da ci gaban duniya.

Hakazalika, cikin nasu jawabi, shugaba Jacob Zuma, shugaba Dilma Rousseff, shugaba Putin da kuma firaminista Manmohan Singh, sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, harkar gudanar da hada-hadar kudin cikin shekarun da dama da suka gabata, ta ci gaba da kawo barazana ga yanayin tattalin arzikin kasa da kasa, shi ya sa, ya kamata kasashen BRICS su karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu, ta hanyar fuskantar kalubale tare, da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya cikin daidaituwa na dogon lokacin. A sa'i daya kuma, sun bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS da MDD da kuma G20.

Yayin taron, shugabannin kasashen BRICS sun kuma tsai da kudurin kafa bankin raya kasashen BRICS da kuma shirya kafa bankin ajiyar kudaden musaya na kasashen BRICS.

An kuma samar da 'sanarwar karshen taron Durban' wadda ta kunshi shirye-shiryen kasashen BRICS, aka kuma sanar da kiran taron BRICS karo na shida a kasar Brazil a shekarar 2014. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China