in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya halarci shawarwari tsakanin shugabannin kasashen BRICs da na kasashen Afirka
2013-03-28 08:38:57 cri

A ranar 27 ga wata da yamma, an gudanar da taron shawarwari tsakanin shugabannin kasashen BRICs da na kasashen Afirka a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, taron da ya samu halartar shugaban kasar Sin Xi Jinping, da kuma takwarorinsa na kasashen Afirka ta Kudu, da Brazil, da Rasha da kuma Indiya. Ragowar shuwagabannin da suka halarci taron sun hada da na Senegal da Chadi, da Angola, da Cote d'Ivoire, da Benin, da jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Sai kuma shuwagabannin Mozambique, da Uganda, da Equatorial Guinea, da Guinea Bissau, da Masar da kuma Habasha.

Shugabannin sun yi shawarwari bisa jigon "bunkasa karfin Afirka: hadin gwiwar kasashen BRICs da na Afirka ta fannin manyan ababen more rayuwa", inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, Sin na nuna goyon bayanta ga raya huldar abokantaka tsakanin kasashen BRICs da kasashen Afirka, kuma ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen BRICs su yi kokarin bunkasa hadin gwiwa da kasashen Afirka, ta fannin raya manyan ababen more rayuwa.

Har wa yau, a madadin gwamnatin kasar Sin, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasarsa na son kulla huldar hadin gwiwa da kasashen Afirka, ta fannin raya manyan ayyukan more rayuwa.
Wannan ra'ayi na shugaba Xi ya dace da na ragowar shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar ta BRICs, kamar dai yadda suka bayyana hakan cikin jawabansu.

Su kuma a nasu bangaren, shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, Afirka nahiya ce da ke da makoma mai haske, wadda kuma ke bukatar gaggauta raya manyan ababen more rayuwa, da kara dunkulewarta, da bunkasa masana'antunta, a yayin da saurin bunkasuwar kasashen BRICS ke samar da babban zarafi ga kasashen na Afirka. Kasashen Afirka na fatan kulla huldar hadin gwiwa da kasashen BRICS, haka kuma suna fatan kara inganta hadin gwiwa da kasar Sin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China