in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana'antun Sin sun taimaka wajen aikin raya tattalin arzikin kasar Afrika ta Kudu
2013-03-27 17:52:57 cri






A matsayinsu na mambobin kasashen kungiyar BRICS, kasashen Sin da Afrika ta Kudu sun inganta dangantakar hadin gwiwa ta tattalin arziki da cinikayya da ke tsakaninsu. Masana'antun kirkire-kirkire na kasar Sin da dama sun shiga Afrika ta Kudu don bude harkokinsu a wurin, inda hakan ya taimakawa aikin raya zamantakewar al'umma da tattalin arziki.

A wata masana'antar kera motoci da ke birnin Johannesburg da ke kasar Afrika ta kudu, 'yan kwadago na kasar Afrika ta Kudu, suna ta harhada motoci a wurin. Idan ba an gaya maka ba, ba za ka san cewa, wannan masana'anta, wata masana'antar kasar Sin ce, sabo da babu basine ko guda a wurin. Injiniya Bomer ya yi shigar tufafin kamfanin FAW na kasar Sin, kuma ya yi shekaru biyar yana aiki a wurin. Ya ce, "Ina son aiki a wannan wuri, sabo da na koyon abubuwa da dama. Haka kuma, ina alfahari don zama memban kamfanin FAW na kasar Sin, yayin da na ga manyan motocin da na harhada sun yin tafiye-tafiye a kan hanyoyi, wallahi, ina jin alfahari."

Kamfanin FAW ya zama daya daga cikin manyan kamfanonin da suka yi gaba-gaba, wajen shiga kasuwannin kasar Afrika ta Kudu. A shekarar 1994, yayin da kamfanin FAW ya shiga kasar, yana cinikin motoci ne kawai, amma yanzu, kamfanin FAW ya kafa wata masana'anta da ke harhada manyan motoci sama da 500 a ko wace shekara a birnin Johannesburg wato cibiyar tattalin arziki ta kasar.

Manajan kamfanin FAW dake kula da harkokin Afrika ta Kudu Liu Xia ya fada wa wakilinmu cewa, yanzu, kamfanin FAW na gina sabon sansanin kirkire-kirkire a tashar ruwa ta Elizabeth dake wurin, kuma an kimanta cewa, bayan da aka kammala aikin gine-gine da saka jari, yawan manyan motocin da za a kera zai kara karuwa, ya ce, "Muna son kara yawan manyan motocin da za a kera, dole ne a gina wata sabuwar masana'anta. A sabuwar masana'antar da ke tashar ruwa ta Elizabeth, ba ma kawai za a samar da motoci ga kasar Afrika ta Kudu ba ne, za a samar da motoci ga kasuwannin kasashen Afrika, an kimanta cewa, za a samar da manyan motocin da yawansu ya kai 5000 a ko wace shekara."

Kasashen Sin da Afrika ta Kudu, kasashen ne da ke samun bunkasuwa sosai, a cikin 'yan shekarun nan, sun kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da ke tsakaninsu, kana Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya mafi girma ta kasar Afrika ta Kudu. Haka kuma, manyan masana'antun kirkire-kirkire na kasar Sin sun shiga kasar Afrika ta Kudu bi da bi, wakilin asusun kula da raya kasar Sin da kasashen Afrika da ke kasar Liu Zhengyi ya gaya wa wakilinmu cewa, Afrika ta Kudu gamayyar tattalin arziki ce mafi girma ta kasashen Afrika, kuma sabo da kyawawan kasuwanni da fiffikon matsayin kasar, Afrika ta Kudu ta jawo hankalin masana'antun kasashen waje sosai, ya ce,"Afrika ta Kudu, kasa ce da ke da manyan ababen more rayuwa, da kasuwanni, da tsarin siyasa mai kyau a kasashen Afrika, kuma yanzu tana kokarin sauya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, sabo da haka, masana'antun kasar Sin suna da babbar damar saka jari a kasar."

Bisa kokarin da masana'antun kasar Sin suka yi a wurin, wasu masana'antun kirkire-kirkire da dama na kasar Sin sun samu karbuwa.

Bayan da masana'antun kirkire-kirkire na kasar Sin suka bude ayyukansu a kasar Afrika ta Kudu, wasu mutane sun nuna damuwa cewa, ko Sinawa za su kwace ayyukan al'ummar kasar Afrika ta Kudu. Amma, bisa shaidu da aka bayar game da bunkasuwar wasu masana'antun kasar Sin suka samu, Sinawa ba su kwace ayyukan kasashen Afrika ba, a maimakon haka, bayan da kamfanonin kasar Sin suka habaka a kasar, sun samar da guraben aikin yi ne a kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China