in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka na bukatar kara samun fahimtar juna yayin da suke hada kai ta fuskar tattalin arziki da cinikayya
2013-03-28 16:04:30 cri






A shekaru 10 da suka wuce, sakamakon kyautatuwar tsarin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka a kai a kai, ya sa saurin hauhawar jimillar cinikayya da ke tsakanin bangarorin 2, ya karu da kashi 28 cikin dari a ko wace shekara. A shekarar 2012 da ta gabata ne jimillar ta wuce dalar Amurka biliyan 200. Sabili da saurin karuwar jimillar, Sin da Afirka suna ta fadada hanyoyin yin hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, inda kuma masana'antu masu zaman kansu da 'yan kasuwa masu zaman kansu suke kara taka muhimmiyar rawa wajen zuba wa juna jari tare da yin cinikayya, lamarin da ya sanya su kara tuntubar takwarorinsu na wurin da kuma al'ummar wurin.

Wadannan 'yan kasuwan da suka fito daga kasashen Afirka da Sin suna yin cinikayya a Sin da Afirka, suna ta fadada hanyoyin ciniki a bangarorin 2. Kuzarin da suke sanyawa da kuma nasarorin da suka samu sun bayyana kyawawan halayensu na yin aiki tukuru ba tare da jin tsoron kome ba. Haka kuma sun bayyana ainihin ma'anar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, wato samun moriyar juna da nasara tare, a kokarin kawo wa jama'ar bangarorin 2 alheri.

Sakamakon karuwar yawan 'yan kasuwan Sin da Afirka a kasashen Afirka da Sin ya sa suke takara da takwarorinsu na wurin tare da hada kai da su.

Ba shakka ana samun sabani a tsakaninsu a wasu fannoni sakamakon bambancin al'adu. Liang Yucheng, mataimakin darekatan cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'ummar kasa ta jami'ar Zhongshan ta birnin Guangzhou yana ganin cewa, ko shakka babu ana samun sabani a zaman yau da kullum yayin da rukunoni 2 suke zama tare, muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne domin samun gurguwar fahimta da rashin cikakkiyar fahimtar juna a tsakaninsu. Ya kuma jaddada cewa, hana tuntubar juna ba zai iya kawar da sabanin ba, a maimakon haka kamata ya yi a kara samun kusanci da al'ummar wurin bisa ka'idar girmama juna, sa'an nan a kara koyon dokokin wurin, da samun masaniya kan kasuwannin wurin, a kokarin inganta samun fahimtar juna a fannonin al'adu da al'adun gargajiya. Kamar yadda mista Liang ya fada, sakamakon karuwar tuntubar juna da cudanyar juna sannu a hankali ya sa za a kawar da sabani.

Takara, wani bangare ne na harkokin kasuwanci. Kamar yadda Nemwel Bosire, shehun malami a fannin ilmin tattalin arziki a jami'ar Presbyterian ta Gabashin Afirka ta kasar Kenya ya fada, dalilin da ya sa kayayyaki kirar kasar Sin ke da rahusa shi ne domin kasar Sin ta yi fice wajen kera kayayyaki. Yawan kayayyakin da kasar Sin take kerawa yana rage kudaden da aka kashewa wajen kera su. Watakila shigowar kayayyaki kirar kasar Sin masu rahusa a Afirka za ta kawo yar illa a harkokin kasuwanci na wurin a cikin gajeren lokaci, amma idan aka yi hangen nesa, za a iya gano cewa, yin takara yadda ya kamata a kasuwa zai kara azama kan aikin kirkire-kirkire. In ana son rage kudaden da a kan kashe wajen kera kayayyaki, to, wajibi ne a yi kokarin kirkire-kirkire. Sa'an nan kuma, masu sayayya na wurin su ne suke fi cin gajiyar irin wannan takara a kasuwa. Masu sayar da kaya suna ta fadada takarar da ke tsakaninsu, lamarin da ya sanya masu sayayya na wurin su iya kwatanta kayayyaki ko hidimomin da ke akwai a kasuwa don sayen mafi inganci da rahusa.

Ko shakka babu akwai sharadi na farko na yin takara yadda ya kamata a kasuwa, wato tabbatar da yin takara cikin adalci. Gwamnatocin Sin da Afirka dukkansu sun tsaya tsayin daka kan ganin 'yan kasuwa sun yi cinikayya bisa dokoki kuma yadda ya kamata. Haka kuma, sau da dama ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bukaci masana'antun kasar Sin da 'yan kasuwa masu zaman kansu da ke zuba jari da gudanar da harkokin kasuwanci a ketare su bi dokokin wurin, yin ciniki ba tare da yin magudi ba, da kawo alheri a wurin.

A yayin taron dandalin tattaunawa mai lakabi da haka "masana'antun kasar Sin a nahiyar Afirka" da aka yi a ranar 18 ga wata, Zhai Jun, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya sake bukaci masana'antun kasar Sin da ke kasuwanci a Afirka su mai da hankali kan ciniki ba tare da yin magudi ba kuma yadda ya kamata.

Haka kuma Mista Zhai ya bukaci wadannan masana'antu su sanya bunkasuwar tasu da bunkasuwar kasashen da suke yin ciniki a wurin tare, su kuma tsara manufar bunkasa kansu bisa manufar raya kasashen Afirka. Kamar yadda mista Zhai Jun ya fada, ko wane dan kasuwa mai hangen nesa kan fahimci cewa, masana'antun su ba za su iya samun dawamammen ci gaba ba har sai sun samu moriyar juna da nasara tare da takwarorinsu da ke kasashen da suke kasuwanci a wurin.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China