in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen BRICS da na Afrika na da makoma mai haske
2013-03-26 18:07:39 cri






Daga ranar 26 zuwa ranar 27 ga wata, za a yi taron karo na 5 na shugabannin kungiyar kasashen BRICS wato Brazil, Rasha, India, Sin, da Afrika ta Kudu a birnin Durban da ke kasar Afrika ta Kudu, inda za a tattauna batun yin hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afrika. Yayin da wani kwararre a fannin tattalin arziki na kamfanin Effient, Dawie Roodt ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, akwai makoma mai haske ga kasashen BRICS da kasashen Afrika.

A cikin 'yan shekarun nan, kasashen Sin, India, Brazil da sauran kasashen BRICS sun inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da kasashen Afrika. A shekarar 2010, a matsayin kasar da ta fi samun ci gaba ta fuskar tattalin arziki a kasashen Afrika. An shigar da Afrika ta Kudu cikin kungiyar kasashen BRICS. Kwararre a fannin tattalin arziki na kamfanin Effient Dawie Roodt ya bayyana cewa, wannan ya nuna cewa, kasashen BRICS sun dora muhimmanci sosai kan kasashen Afrika, ya ce, "Afrika ta Kudu ba wata gamayyar tattalin arziki da ta fi girma ba ce a kasashen duniya, amma me ya sa ta iya shiga kungiyar kasashen BRICS? A ganina, dalilin shi ne an gayyaci kasar Afrika ta Kudu don wakilcin kasashen Afrika."

Shigar da Afrika ta Kudu a cikin kungiyar BRICS, ya sa kasashen BRICS da kasashen Afrika suka iya kara samun damar inganta hadin gwiwa da ke tsakaninsu. Kasar Afrika ta Kudu na da kasuwanni masu kyau da kyakkyawan yanayi a wurin, wanda ya bude kofa ga sauran kasashen BRICS da su samu damar shiga kasuwannin kasashen Afrika da gina kasashen Afrika. Taken shawarwarin da za a yi a wannan karo shi ne "kafa dangantakar abokantaka ta samun bunkasuwa da raya masana'antu da samun hadin gwiwa tare, tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afrika". A tsawon lokacin taron kuma, za a yi taron tattaunawa na shugabannin kasashen BRICS da kasashen Afrika.

Roodt ya bayyana cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da ke tsakanin kasashen Afrika da kasashen BRICS na iya taimakawa juna ta fuskar tattalin arziki, don haka hadin gwiwarsu zai samu makoma mai haske, ya ce, "Kasashen Afrika na da albarkatun ma'adinai da kayayyaki da yawa. Duk da cewa, tattalin arzikin kasashen Afrika bai samu habaka sosai ba, akwai yawan al'umma, da babbar kasuwa a kasashen Afrika, kuma kasashen Afrika suka bukaci kudade da dama don gina hanyoyi, tashoshin ruwa, da gadoji da sauran muhimman ababen more rayuwa, kasashen BRICS za su iya kawo wa Afrika kudade, ciniki, da damar musayar fasahohi da sauransu."

An kafa tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS ne, bayan abkuwar rikicin hada-hadar kudi a kasashen duniya. Idan mun dudduba sakamakon da aka samu a cikin tarurrukan shugabannin kungiyar kasashen BRICS a baya, muna iya gano cewa, ba ma kawai kasashen BRICS sun mai da hankali game da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya ba, haka kuma sun daidaita matsayin da suka kai, inda suka yi kira da a yi gyare-gyare game da tsarin hada-hadar kudi na duniya, da kara ikon kasashen da suke samun ci gaba sosai ta fuskar bayyana ra'ayoyinsu. Ban da wannan kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, domin karfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya da ke tsakanin kasashen kungiyar BRICS, kasashen BRICS sun riga sun cimma matsaya guda kan yadda za a samar da kudade don kafa bankin samun bunkasuwa tare, kuma ana sa ran tabbatar da wannan labari a yayin taron.

Dawie Roodt ya yi sharhi cewa, nan ba da dadewa ba, za a kafa bankin kungiyar kasashen BRICS. Ya ce, "Idan kasashen yammacin duniya ba su fatan so ikonsu dake asusun ba da lamuni na duniya da bankin duniya ga kasashen da suke samun saurin bunkasuwa sosai ba, to, wadannan kasashe za su yi la'akari da inganta hadin gwiwarsu wajen kafa wata hukumar kudi irin haka. Na yi imani cewa, nan ba da dadewa ba, za a samu bankin samun bunkasuwa na kasashen BRICS, wanda zai taka muhimmiyar rawa, ba ma kawai tsakanin kasashen BRICS ba, hattama zai yi tasiri ga sauran kasashen da suke samun bunkasuwa sosai da dukkan kasashen duniya baki daya."

Haka kuma ya ba da shawara cewa, domin kara yin takara da kasashen yammacin duniya, kamata ya yi kasashen BRICS su inganta kafuwar tsarin hada-hadar kudi. Yayin da yake tabo maganar makomar tsarin kungiyar kasashen BRICS, Roodt ya bayyana cewa, ana sa ran ganin shigar da wasu karin kasashe cikin kungiyar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China