in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari tsakanin shugabannin kasar Sin da Afrika ta kudu.
2013-03-26 16:35:56 cri
Yau Talata 26 ga wata a birnin Pretoria na kasar Afrika ta kudu, shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ya kai ziyara a kasar ya yi shawarwari tare da mai masaukinsa shugaba Jacob Zuma, inda suka yi musayar ra'ayi kan yadda za su zurfafa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukan fannoni.

Shugaba Zuma ne dai ya tarbi Xi Jinping cikin farin ciki domin nuna maraba da ziyarar tasa.

Mr Xi ya isa kasar a daren ranar 25 ga wata, inda ake sa ran zai halarci ganawa karo na biyar na shugabannin kasashen BRICS da za a yi daga ran 26 zuwa 27 a birnin Durban na kasar.

Hakazalika, Mr Xi ya bada jawabi a filin saukar jiragen saman kasar ta Afirka ta Kudu, yana mai kyakkyawan fatan cimma nasarar shawarwari da zai yi da shugabannin kasar Afrika ta kudun, ciki hadda Jacob Zuma dangane da wasu batutuwa da suka shafi dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da wasu batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da suka jawo hankalin bangarorin biyu.

Dadin dadawa, ya yi imanin cewa, za a cimma nasara cikin wannan ziyara, karkashin kokarin da bangarorin biyu suke yi tare, da zurfafa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China