Wannan rahoto mai taken 'kasashen BRICS da Afirka' ya nuna cewa, cikin kasashe 20 da suke kan gaba a jerin kasashe da suka fi zuba jari kai tsaye a Afirka, wato idan aka yi nazari kan fannin musayar kudi wajen zuba jari ke nan, za a iya ganin cewa, kasashen Sin, India, da Afirka ta Kudu suna kan matsayin na hudu, biyar da kuma sha bakwai, kana, idan aka juyo kan ajiyar kudi, kasashen Afirka ta Kudu, Sin, India da kuma Rasha suna matsayi na biyar, shida, bakwai da kuma sha biyar.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, fannonin da kasashen BRICS suka fi mai da hankula wajen zuba jari a Afirka su ne, sana'o'in kira da hidima, wadanda suka ba da babbar gudumawa wajen samar da karin guraben aikin yi da kuma bunkasa tattalin arziki a kasashen Afirka. (Maryam)