in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jaddada wajibcin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika
2013-03-25 20:01:18 cri






Shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda yake kai ziyarar nahiyar Afrika ya ba da wani jawabi a yau Litinin 25 ga wata mai jigon "Raya sahihiyar dangantakar abokantaka ta sada zumunci tsakanin Sin da Afrika", inda a cikin jawabinsa Mr Xi ya takaita fasahohin da aka samu wajen bunkasuwar bangarorin biyu irin ta sada zumunci cikin dogon lokaci tare da jaddada cewa, Sin da Afrika sun kasance wata kungiya da ke da muradu da moriya bai daya. A cikin wannan sabon yanayi, Sin za ta ci gaba da zurfafa dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afrika.

A safiyar yau ranar 25 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabinsa a zauran mahawara na Nyerere dake birnin Dares Salaam na kasar Tanzaniya, inda da farko ya yi gaisuwa da harshen Kiswahili. Ya ce:"Habari,habari, ina farin cikin saduwa da ku a yau a babban wannan zaure."

Wannan ziyara ta kasance ta farko da Xi ya kai a nahiyar Afrika bayan ya kama mukaminsa na shugaban kasar Sin, kuma karo na shida ke nan da Xi ya sa kafa nahiyar Afrika. A cikin jawabinsa, da farko ya bayyana abubuwa da ya gani da yadda aka tarbe shi cikin himma a yayin ziyararsa a nahiyar Afrika, kuma ya nuna mamaki sosai ga yadda kasashen Afrika suke samun bunkasuwa cikin sauri da kuma nuna jin dandinsa ga yadda kasashen Afrika suke bayyana sahihin zumunci ga jama'ar kasar Sin.

Mr Xi ya waiwayi ci gaban da bangarorin biyu suka samu wajen zurfafa zumunci dake tsakaninsu tare da jaddada cewa, an kwashe shekaru da dama ana raya dangantaka tsakanin Sin da Afrika, tare da tinkarar kalubaloli da kuma warware matsalolin dake shafar bangarorin biyu cikin hadin gwiwa. Hakazalika bangarori biyu kuwa na nacewa ga akidar raya dangantakar dake tsakaninsu bisa tushen mutunta juna, kawo moriyar juna da samun bunkasuwa tare. Mr Xi ya ce:

"Sin da Afrika na da matsaya guda saboda sun taba fuskantar kalubale irin daya, har ma dake tattare da muradun raya kasa da moriya bai daya. Sin da kasashen Afrika na tsaya tsayin daka kan mutunta matsayin da suka dauka. Kuma suna nuna wa junansu goyon baya dangane da wasu batutuwa dake shafar muhimmiyar moriya dake da daraja ga bangarorin biyu. Ban da haka, muna hagen nesa a duk wani muhimmin lokaci na raya dangantakar dake tsakaninmu tare kuma da neman sabuwar bunkasuwar hadin gwiwa ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu yadda ya kamata."

Xi Jinping kuma ya kara da cewa, yau nahiyar Afrika ta zama daya daga cikin wasu yankuna da suke fi samu bunkasuwar tattalin arziki a duniya, kasar Sin kuwa tana ci gaba da samu bunkasuwa yadda ya kamata, dalilin da ya sa bangarorin biyu suke fuskantar sabon zarafi mai kyau wajen raya dangantakar dake tsakaninsu. Mr Xi ya bayyana yadda Sinawa za su raya dangantakar dake tsakaninsu da jama'ar Afrika bisa wata kalma ta sahihanci. Kuma yana jaddada cewa, Sin sahihiyar kawa ce ga nahiyar Afrika har abada, kuma ba za ta canja wannan matsayin da take dauka ba duk da cewa za ta ci gaba da samun karin bunkasuwa da daga matsayinta cikin duniya. Sin na nacewa ga samu bunkasuwa tare da kasashen Afrika, Sin za ta cika alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika. Kuma game da sabbin matsaloli da za su bullo cikin hadin gwiwa da za su yi, Sin za ta warware su yadda ya kamata bisa ka'idar mutunta juna da kawo moriyar juna. Game da wannan batu, Mr Xi ya ce:"Sin za ta ci gaba da hada kai tare da kasashen Afrika ta fuskokin zuba jari da tattara kudi da kuma tabbatar da ba da rancen kudi da yawansa ya kai dala biliyan 20 cikin shekaru uku masu zuwa. Tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwa a fannonin ayyukan noma, sha'anin kikire-kikire da sauransu, har ma da taimakawa kasashen Afrika yin amfani da zarafinsu mai kyau wajen samun bunkasuwa yadda ya kamata ta yadda kasashen Afrika za su dogaro da karfin kansu. Kasar Sin kuma za ta taimakawa kasashen Afrika wajen horar da kwararru a dukkanin fannoni da yawansu zai kai dubu 30 cikin shekaru uku masu zuwa har ma da samar da guraben samun ilmi tare da samun kudin bonas dubu 18. Ban da haka, Sin za ta karfafa ayyukan isar da fasahohi ga kasashen Afrika da kuma cin gajiyar su tare da kasashen Afrika. Dadin dadawa, Sin za ta samar da taimako yadda ya kamata ga kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa ba tare da gitta wani sharadin siyasa ba."

Budu da kari, a cikin jawabin nasa, Xi Jinping ya bayyana fatansa na raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, yana mai cewa, ya kamata, duk wata kasa ta mutunta ikon mulkin kasashen Afrika. Shi ma ya nuna kyakkyawar fata ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu a nan gaba. Ya ce:"Sin za ta mai da kasashen Afrika sahihan kawayenta duk da cewa za ta samu babbar bunkasuwa nan gaba. Sin ba za ta samu bunkasuwa kashin kanta ba, sai ta yi dogaro da karfin duniya da ma Afrika. Ban da haka, tabbatar da wadata da zaman karko a duniya da na Afrika na bukatar taka rawar kasar Sin. Ko da yake, akwai nisa tsakanin Sin da Afrika, amma duk suna mai da hankali kan juna." (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China