Bisa tsarin ziyarar shugaba Xi, zai tattauna da takwaransa na Tanzania Mrisho Kikwete kan muhimman batutuwan da suka shafi dangantakar dake tsakanin kasashen nasu, inda kuma daga bisani shugabannin biyu za su rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi na hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da kuma musayar al'adu.
Kasar ta Tanzania ce dai ta biyu baya ga Rasha a jerin kasashen da shugaba Xi ya ziyarta tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Sin a farkon wannan wata na Maris da muke ciki. (Saminu)