in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta nace ga matsayin samun bunkasuwar duniya cikin lumana, in ji shugaban kasar
2013-03-20 16:52:05 cri






Sabon shugaban kasar Sin Xi Jinping zai fara ziyararsa ta farko bayan ya hau kan mukaminsa zuwa ga kasashen Rasha, Tanzaniya, Afrika ta kudu da Kongo Brazzaville a wannan mako, tare kuma da halartar dandali karo na biyar na shugabannin kasashen BRICS. Wannan ziyara ta Xi Jinping za ta jawo hankalin kasa da kasa kwarai. A ran 19 ga wata kuma, a yayin da Xi ke zantawa da manema labaru na kasashen BRICS, ya jaddada matsayin da Sin take dauka na tuntubar juna kan ci gaban da ake samu a fannin kimiyya da fasaha da bunkasuwar duniya mai jituwa da wadata.

A yayin taron manema labaru da aka yi a ran 19 ga wata, Mr Xi Jinping ya yi nuni da cewa:

"Ina farin ciki yin hira da ku, kuma ina gaida ku. Zan fara ziyarata nan da kwanaki uku masu zuwa, ta wannan hanya ce zan nuna sahihiyar gaisuwata ga jama'ar duniya, kuma ta kasance ziyara ta farko a cikin wa'adina, ina fatan kara sada zumunci tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasa da kasa, da kuma kara hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da samun moriyar juna, har ma da sa kaimi ga bunkasa tsarin hadin kai tsakanin kasashen BRICS yadda ya kamata."

A safiyar wannan rana, Mr Xi ya zantawa da manema labaru na kasashen BRICS wato Sin, Rasha, Afrika ta kudu, Indiya, Brazil. A cikin awa daya da rabi, 'yan jarida guda 10 sun gabatar da tambayoyinsu da suka shafi wannan batutuwa, ciki har da batun dangantaka tsakanin Sin da Rasha da kuma nahiyar Afrika, taron shugabannin kungiyar BRICS da za a yi a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu, batun yadda Sin za ta kara gyare gyare domin bunkasuwa, da kuma dangantakar tsakanin Sin da duniya. Bugu da kari, wadannan 'yan jarida sun aza tambayoyinsu dangane da aikin shugaba Xi da zaman rayuwarsa. Wadannan tambayoyi sun nuna cewa, kasa da kasa na sanya muhimmanci sosai kan sabuwar gwamnati da makomar samun cigaban kasar Sin.

Rasha ta kasance zangon farko na ziyarar Xi Jinping a wannan karo, wanda ya bayyana muhimmancin da Sin take dauka kan dangantakar dake tsakaninta da Rasha. Mr Xi ya ce:

"Kasashen Sin da Rasha suna kasancewar muhimman abokan juna wajen yin hadin gwiwa. Ya kamata, kasashen biyu su kara amincewa da juna ta fuskar tsare-tsare da siyasa, har ma daure juna gindi kan batutuwan da suka shafi moriyar kasashen biyu. Har ma da kara hadin gwiwa da zurfafa mu'ammala haka kuma da kara daidaita yin hadin kai cikin harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya."

Mr Xi Jinping zai kai ziyara a kasashen Afrika gudu uku dake kudu da Sahara a wannan karo. Game da batun bunkasuwar dangantakar tsakanin Sin da Afrika cikin sauri, Mr Xi ya ce:

"Sin da Afrika suna yin hadin kai a dukkanin fannoni, Sin kuma na dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar sada zumunci dake tsakaninta da dukkanin kasashen Afrika ba tare da nuna bambanci ba. Sin da kasashen Afrika kasashe ne masu tasowa, suna da moriya bai daya, hakan ya sa, ya kamata, Sin na fatan kara hadin gwiwa da kawo moriyar juna da ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba a dukkan fannoni, ta yadda za a amfanawa jama'arsu."

Za a yi ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS a birnin Durban a karshen wannan wata da muke ciki. Ana mai da hankali sosai kan ra'ayin kasar Sin. Mr Xi kuma ya bayyana ra'ayinsa kan dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen duniya. Ya ce:

"Sau da dama ne, Sin ta yi alkawari cewa, za ta nace ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana ba tare da daukar manufar kama karya ba. Sinawa na tsaya tsayin daka kan matsayin daukar alhakin dake wuyanta baki daya ba tare da nuna bambanci ba. Yana fatan kasa da kasa su yi mu'ammala yadda ya kamata, da kuma koyi da juna da samun bunkasuwa tare. Haka kuma da tumtubar juna bisa ci gaban da suka samu a fannin kimiya da fasaha ta yadda duniya za ta samu ci gaba baki daya. Sannan kuma da mutunta burin jama'a da samun bunkasuwar duniya mai jituwa da wadata cikin lumana."

'Yan jarida sun gamsu da amsoshin da Xi Jinping ya bayar, tare kuma da nuna kyakkyawar fata ga ziyarar da Xi Jinping zai yi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China