in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan Afrika ta Kudu yana fatan taron BRICS zai karfafa zumunci da Afrika
2013-03-20 11:04:52 cri

Wani minista a kasar Afrika ta Kudu ya ce, yana fatan taron kasashen kungiyar BRICS wato kasashe biyar na Brazil, Russia, Indiya, Sin da kuma Afrika ta Kudu da za'a bude kwannan nan zai samar da wata dama na inganta dangantaka da hadin gwiwa tsakanin kasashen da nahiyar Afrika baki daya.

Marthinus Van Schalkwyk wanda shi ne ministan yawon shakawata, ya ce, wannan taron shi ne karo na farko da za'a yi a nahiyar Afrika, don haka, ya wajaba a mai da hankali kan yadda za'a inganta dangantaka tsakanin nahiyar baki daya da mambobin kasashen kungiyar.

Mr. Van Schalkwyk ya ce, muhimman bayanan da za'a tattauna a wajen wannan taron sun hada da batun kafa babban bankin da zai lura da cigaban kasashen mambobin, sannan kuma za'a kammala tattaunawa a kan wani kwamiti na kasuwanci domin inganta cinikayya da zuba jari.

Ministan ya ce, hadin kan tattalin arziki a taron BRICS zai kuma kawo wani muhimmin matsayi ga cigaba a fannin yawon shakatawan kasar, inda ya yi bayanin cewa, ministocin yawon shakatawar wadannan kasashen BRICS za su gana kafin babban taron domin tattauna yadda za su fadada tare da inganta hadin gwiwa a wannan fannin na yawon shakatawa.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China