in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta dage kan hanyar raya kasa cikin lumana, in ji shugaban kasar
2013-03-19 19:03:06 cri

Kafin shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fara ziyararsa a kasashen Rasha, Tanzania, Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Congo, sannan kuma ya isa kasar Afirka ta Kudu domin halartar taron shugabannin kasashen BRICS, wato kasashe 5 da suka hada da Brazil, Rasha, India, China, da Afirka ta Kudu, wadanda ke samun saurin karuwar tattalin arziki, shugaba Xi ya yi hira da wasu manema labaru daga kafofin watsa labarun kasashen BRICS a nan birnin Beijing a ranar Talata 19 ga wata. Inda a lokacin, ya bayyana manufofin kasar Sin a fannonin huldar dake tsakanin Sin da Afirka, hadin gwiwar kasashen BRICS, da matakan gyare-gyaren dake gudana a nan kasar Sin.

Dangane da batun huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu, Xi Jinping ya bayyana cewa, sakamakon kulla huldar diplomasiyya shekaru 15 da suka wuce, kasashen 2 sun riga sun zama kawaye a bangaren hadin gwiwa da juna a fannoni daban daban wanda kuma ya shafi manyan tsare-tsare.

A cewar Mista Xi, kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu sun kasance kasashe masu sabbin kasuwanni, da wadanda ke samun tasowar tattalin arziki, sa'an nan suna kallon wannan hulda a matsayin wata damar samun ci gaba, da abun dogara a fannin hulda da kasashen waje, don haka hadin kan kasashen 2 na kara samar da babban tasiri a duk fadin duniya.

Ban da haka, a fannin huldar dake tsakanin bangarorin Sin da Afirka, Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka dukkansu sun kasance kasashe masu tasowa wadanda ke samun moriyar bai daya sosai. Don haka hadin gwiwar da ke gudana tsakanin bangarorin 2 ta shafi fannoni daban daban, tare da amfanawa dukkan bangarorin 2. Kasar Sin ba za ta manta da yadda kasashen Afirka suka taba goyon bayanta ba a manyan batutuwan da suka shafi moriyar kasarta. Don haka duk wani yanayin da ake ciki a duniya, kasar Sin za ta dage kan mara wa kasashen Afirka baya a kokarinsu na neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, da cigaban tattalin arziki, da walwala, da yunkurin dunkulewa waje daya, da shiga harkokin duniya tare da samun daidaituwa.

A bangaren hadin gwiwar da ake yi a tsakanin kasashen BRICS kuwa, Xi Jinping ya ce, hadin gwiwar yana da amfani ga samun daidaituwa tsakanin tattalin arzikin duniya, da kyautata fasahar kula da duniya, da kokarin tabbatar da tsarin dimokuradiya a harkokin kasa da kasa. Don haka kasar Sin na fatan ganin taron da za a shirya a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu zai gabatar ma kasashen duniya wasu bayanai masu yakini, wanda zai sa su zama tsintsiya madaurinki daya, a kokarin hadin kai, da tabbatar da moriyar juna.

Kan batun huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen duniya kuwa, Mr Xi ya ce, yayin da kasar Sin ke samun karin karfin tattakin arziki, za ta kara daukan nauyi a harkokin kasa da kasa gwargwadon karfinta, don samar da karin gudummowa ga zaman lafiya da ci gaban bil Adama. Kana kasar Sin za ta tsaya kan hanyar neman samun ci gaba tare da kiyaye zaman lafiya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China