in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na Sin ya ki amincewa da salon irin mulkin mallaka da shugaban bankin tsakiya na Nijeriya ya zargi kasar Sin
2013-03-19 16:16:51 cri






A makon jiya, shugaban bankin tsakiya na kasar Nijeriya Sanusi Lamido Aminu Sanusi ya bayar da wani sharhi a jaridar Financial Times, inda ya ce, kasar Sin na gudanar da wani sabon salon mulkin mallaka a nahiyar Afirka. Game da wannan batu, manzon musamman na kasar Sin mai kula da harkokin nahiyar Afirka Zhong Jianhua ya bayyana a birnin Abuja dake kasar Nijeriya a ranar 18 ga wata cewa, bai amince ba da ra'ayin sabon salo na mulkin mallaka da ake zargin kasar Sin da ta yi, ko shakka babu kasashen Afirka da kasar Sin za su samu ci gaba cikin daidaici.

Shugaban bankin tsakiya na kasar Nijeriya Sanusi Lamido Aminu Sanusi ya bayar da wani sharhi a jaridar Financial Times a ranar 12 ga wata, inda ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Afirka su kawar da kyakkyawan begen da suke nunawa kasar Sin, su san cewa kasar Sin abokiyar hadin gwiwa ce, kana muhimmiyar kasa ce da kasashen Afirka suke iya yin takara da ita a duniya. Watakila kasar Sin na gudanar da wasu ayyukan mulkin mallaka kamar yadda wasu kasashe suka yi a da a nahiyar Afirka.

Game da wannan, manzon musamman na kasar Sin mai kula da harkokin nahiyar Afirka Zhong Jianhua ya bayyana cewa, bai amince ba da irin wannan ra'ayi. Ya ce, kasashen Afirka sun fuskanci da fama da mulkin mallaka a cikin dogon lokaci, an sace albarkatun nahiyar Afirka da dama, lamarin da ya haddasa talauci a nahiyar yanzu. Kamata ya yi 'yan nahiyar Afirka su fahimci mene ne hakikanin ma'anar mulkin mallaka. Ya ce,"A lokacin da, kasar Nijeriya ta fuskanci matsaloli da dama yayin da take kokarin zuba jari ga masana'antu da gudanar da ayyukan more rayuwa. Amma a halin yanzu, kasar ta iya biya bukatun rayuwar jama'a yadda ya kamata, kana ta yi amfani da kudin jari wajen inganta masana'atun kasar. wannan ya bayyana babban canjin da ake samu a nahiyar Afirka. Ya kamata a fahimci mene ne ainihin mulkin mallaka."

Hakazalika Zhong Jianhua ya jaddada cewa, ban da ra'ayin mulkin mallaka da aka zargi kasar Sin, akwai wasu abubuwa masu yakini a cikin wannan sharhi, wato ya bayyana cewa, kasashen Afirka suna son yin takara tare da kasar Sin. Zhong Jianhua ya ce,"A farkon lokacin da aka gudanar da manufar yin kwaskwarima a kasar Sin, an rufe kamfanoni da dama a kasar, ma'aikatu fiye da miliyan daya sun rasa ayyuka. Wannan ya kasance babban kalubalen da kasar Sin ta fuskanta. Amma kasar Sin ta dauki matakai wajen tinkarar shi. An fara shiga takara tare da kamfanonin ketare na sauran kasashen duniya, da koyi fasahohi daga wajensu. Nasarorin da kasar Sin ta samu sun zo daga irin wannan takara."

Ban da wannan kuma, Zhong Jianhua yana fatan kasashen Afirka za su yi takara tare da kasar Sin, har ma yin takara tare da sauran kasashen duniya. Ta haka za a sa kaimi ga samun ci gaban kasashen Afirka, kana za a taimakawa dukkan duniya wajen samun bunkasuwa tare. Zhong ya ce,"Ina fatan kasar Nijeriya za ta shirya tinkarar kalubale, kuma mu yi maraba da ita wajen yin takara tare da kasar Sin. Ina fatan kasashen Afirka za su cimma nasarar wannan takara a duniya, domin wannan ya bayyana cewa, kasashen Afirka za su iyar samun ci gaba bisa karfin kansu. Na mai da irin wannan hali a matsayin halin samun moriyar juna, saboda ba wanda zai ci tura a takarar. Idan kasashen Afirka suka samu ci gaba, za a kawo babbar dama ga kasar Sin, har ma ga dukkan duniya, kuma za a sa kaimi ga bunkasuwar duniya gaba daya." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China