in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afrika sun tattauna matakan da za su dauka don inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu
2013-03-19 16:09:10 cri






A jajibirin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasashen Afrika, a ranar 18 ga wata da yamma, kwamitin kula da harkokin diplomasiyya tsakanin jama'a na kasar Sin ya shirya wani taron tattaunawa da ke da taken "Masana'antun Sin a kasashen Afrika" a nan birnin Beijing, inda jami'an diplomasiyya na kasar Sin da kasashen Afrika, da 'yan kasuwa da kwararru suka tattauna kan matakan da za'a dauka don inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Yanzu, ga abokin aikina Bako da karin bayaninsa.

Bisa shirin da ma'aikatar harkokin wajen Sin ta bayar, an ce, a karshen wannan wata, sabon zababben shugaban kasar Sin Xi Jinping zai fara ziyararsa a kasashen waje, bayan hayewa ragamar mulkin kasar. Ban da ziyara a kasar Rasha, shugaban na Sin zai ya da zango a kasashen Afrika gudu 3. Mahalartar taron sun bayyana cewa, wannan ya nuna cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai game da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kana kuma ya nuna muhimmancin wannan dangantaka ga bangarorin biyu. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhai Jun ya bayyana cewa, yanzu, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta shiga wani lokaci na samun bunkasuwa cikin gaggawa , kuma hakikanin hadin gwiwar bangarorin biyu ya samu babban ci gaba, ya ce, "Tun daga shekarar 2009, Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen Afrika, kuma jimillar kudin cinikayya da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta karu daga dalar biliyan 10 a shekarar 2000, zuwa kusan dalar biliyan 200 a shekarar 2012. Haka kuma, a yanzu, kasashen Afrika sun zama kasuwanni na biyu da kamfanonin Sin suke samun ayyukan kwangila, kuma su ne wurin saka jari na 4 da kamfanonin Sin suka je suka fara sana'o'insu. Haka kuma ya zuwa watan Afrilu na shekarar 2012, yawan jarin da Sin ta saka a kasashen Afrika kai tsaye ya tasam ma dalar Amurka biliyan 15.3."

Ban da wannan kuma, Zhai Jun ya ci gaba da bayyana cewa, duk da cewa, yawan kudin da aka samu wajen yin hadin gwiwa tsakaninsu ya karu sosai, har yanzu, akwai kalubale sosai wajen kyautata ingancin hadin gwiwa a tsakaninsu. Masana'antun Sin ba su dade ba da fara saka jari a kasashen waje, don haka ba su kware ba wajen raya sana'o'insu a kasashen waje. Sabo da haka, kamata ya yi su ci gaba da koyon ilmin raya sana'o'i a kasashen waje, tare da daukar alhakin da ke bisa wuyansu. Game da wannan, Zhai Jun ya ba da shawarwari ga kamfanonin Sin da suke saka jari a kasashen waje, ya ce, "Yanzu kasashen Afrika sun mai da hankali sosai game da inganta kwarewa wajen raya sana'o'insu, da kokarin raya masana'antu da kansu, don kyautata zaman rayuwar al'ummarsu, sabo da haka, suna fatan karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kasar Sin a fannonin manyan kayayyakin more rayuwa, aikin gona, kirkire-kirkire, makamashi, horaswa da dai sauransu. Kamata ya yi masana'antun Sin su yi la'akari da inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu da kasashen Afrika a wadannan fannoni."

Ban da shawarwarin da kasar Sin ta bayar game da hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, su ma wakilan kasashen Afrika da suka halarci taron, sun ba da shawarwarinsu, inda karamin jakadan kasar Afrika ta Kudu da ke kasar Sin ta fuskar tattalin arziki Thembinkosi Gcoyi ya bayyana cewa, kasashen Afrika suna sa rai sosai game da jarin da masana'antun Sin suka saka, don haka kamata ya yi, wannan jari ya yi amfani wajen kyautata kwarewar kasashen Afrika wajen raya sana'o'insu, ya ce, "Dole ne masana'antun Sin su tuna da cewa, kamata ya yi ayyukan da suka yi a kasashen Afrika sun yi amfani ga raya kasashen Afrika, sabo da kasashen Afrika su ma suna fatan raya masana'antunsu, suna bukatar masana'antun Sin da su samar da fasahohi gare su, da horar da kwararru, ta hakan ne, za a raya tattalin arzikin kasashen Afrika."

Game da zargin da kasashen yammacin duniya suka yi wa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wakilan kasashen Afrika da suka halarci taron ba su amince da wannan ba. Jakadan kasar Tanzaniya da ke kasar Sin Philip S. Marmo ya ce, "kasashen yammacin duniya sun ce, dankon zumunci da ke kasancewa tsakanin Sin da Afrika bai kawo moriyar juna ba, tare da samun rashin amincewa da rashin girmamar juna, ina tsammani wannan ba gaskiya ba ne, kuma ya zama zargi ne marasa tushe, kawai suna son kulla makirci ne."(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China