in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron BRICS karo na 5 wata dama ce domin bunkasa Afrika ta Kudu
2013-03-19 14:09:50 cri

Babban taron kasashen BRICS karo na 5 da za'a bude daga ranar 26 zuwa 27 ga watan Maris a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu, zai kasance wata babbar dama wajen bunkasa cigaban kasar Afrika ta Kudu, a cewar wani sharhin da wani masani ya rubuta a cikin jaridun kasar.

Ranakun 26 da 27 ga watan Maris, Afrika ta Kudu za ta karbi bakuncin taron BRICS karo na biyar a birnin Durban, wanda zai zama muhimmin lokaci ga gwamntin kasar da kuma jam'iyyar ANC dake mulki, in ji jaridar South African Broadcasting Corporation da ta rawaito kalaman mista Saliem Fakir, wani masamin taro a jami'ar Stellebosch.

Kungiyar BRISC na kunshe da manyan kasashen dake tasowa a duniya da suka hada Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu. Wannan shi ne karo na farko da kasar Afrika ta Kudu za ta shirya wannan babban taron BRICS a kasarta, tun bayan shigarta a cikin gungun kasashen BRICS a ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2010. Tun bayan tashin hankalin mahakar Marikana a cikin watan Agustan shekarar 2012, wasu kasashen yammacin duniya suka yi ta kai matsin lamba da nuna yatsa ga jam'iyyar ANC dake mulki kan yadda take tafiyar harkokin albarkatun ma'adinai a kasar, a cewar wannan masani. Dalilin haka ne a 'yan kwanakin baya, shugaba Jacob Zuma ya yi kashedi ga kamfanonin kasashen waje domin su sauya tsarinsu na aiki da kuma dakatar wata manufar nuna mulkin mallaka kan gwamnatocin kasashen Afrika cikin wani kalami dake nuna bacin ransa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China