in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon firaministan kasar Sin ya tabbatar da manufar yin gyare-gyare a gida da samar da alheri ga jama'ar kasar.
2013-03-18 17:30:39 cri






An rufe manyan taruka biyu na bana, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar a jiya Lahadi 17 ga wata, hakan dai ya nuna cewa sabuwar gwamnatin kasar dake karkashin shugabancin firaminista Li Keqiang, ta soma wa'adin aikinta na tsawon shekaru 5. Yayin ganawarsa ta farko da manema labaru a matsayin sabon firaminista kasar ta Sin, Li Keqiang ya bayyana manufofinsa a yayin gudanar da mulki karkashin sabuwar gwamnati a shekaru biyar masu zuwa.

"Yin gyare-gyare a gida", "samar da alheri ga jama'a", "tabbatar da adalci", abubuwa uku ne da suka kasance cikin kalamomin da suka fi burge mutane, yayin da Li Keqiang ke amsa tambayoyin manema labaru na gida da na waje.

Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun taba kiran Li Keqiang, a matsayin "Kwararre a fannin warware manyan matsalolin tattalin arziki da zaman al'umma", hanyar da yake bi ita ce tsayawa tsayin daka kan yin gyare-gyare a gida. A cikin shekaru biyar da suka gabata, wasu gyare-gyaren dake da wuyar gudanarwa, wadanda ke da nasaba da bunkasuwar kasar Sin, da sada jama'a da alherin rayuwa, ciki har da yin gyare-gyare kan muhalli, da kiwon lafiya, da harajin man fetur, da sauransu, dukkansu sun gudana karkashin jagorancin Li Keqiang, kuma an samu cikakkiyar nasarar yinsu.

Tun daga babban taron wakilai na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka shirya a bara kawo yanzu, kalmar da ta kan maimaitu a jawabin Li Keqiang ita ce, "yin gyare-gyare". A yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 17 ga wata, ya kara ambatar "yin gyare-gyare", inda ya nuna cewa, "Abu ne mai wuya a daidaita moriya, amma duk da haka za a gudanar da aikin", ba kawai hakan yana nufin sanya himmar yin gyare-gyare ba ne, a sa'i daya kuma ta nuna niyyar sabuwar gwamnatin ta daukar nauyin shiri, da kawar da wahalhalu daban daban.

A yayin taron manema labarun kuma, Li Keqiang ya yi alkawarin cewa, ba za a kafa sabbin gine-gine na gwamnatoci ba, yawan ma'aikatan gwamnati ba zai karu ba, yawan kudin da gwamnati take kashewa a fannonin shirya liyafa, kiyaye motoci, da ziyarar aiki ba zai karu ba. Bugu da kari, Li Keqiang ya ba da amsa kan tambayoyi game da wasu batutuwan zaman rayuwar jama'a, ciki har da kiyaye muhalli, da ingancin abinci, da kara kudin shiga da sauransu, inda ya amince da matsalolin da ake fuskanta, da kuma yin alkawarin kafa wani tsari, da zai tabbatar da zaman rayuwar jama'a dake dukkan sassan kasar.

Hakan dai ya nuna babbar manufar sabon firaministan don gane da mai da moriyar jama'a a gaban kome, a fagen gudanar da harkokin mulki.

Bayan haka kuma, Li Keqiang ya gabatar da cewa, "kamata ya yi gwamnati ta kasance mai tabbatar da adalci a zaman rayuwar al'umma". Wannan maganar ta nuna cewa, ko shakka babu, ana kara mayar da hankali ga kiyaye adalci, a matsayin muhimmin aikin da gwamnatin ke gudanar cikin ayyukanta. Tun daga shekaru 30 da suka wuce da ake gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, bisa sauyin tsarin zaman al'umma, da bukatu irin daban daban da ake bukata wajen samun moriya, da matsaloli da ake fuskanta suna ta karuwa, hakan dai ya tabbatar da adalci na zama wani aikin gaggawa dake bukatar a ba shi kulawa.

"Sai ta hanyar tabbatar da adalci ne, za a iya gudanar da harkokin kasa yadda ya kamata", saboda haka, kara karfin tallafawa masu fama da talauci, da marasa karfi, tare kuma da inganta samun adalci a zaman al'umma, sun zama muhimmin sashi, a babbar manufar sabuwar gwamnati.

Yanzu, kasar Sin na cikin wani mawuyacin hali na yin gyare-gyare. Sake daidaita moriya, da karuwar fatan da jama'a ke nunawa gwamnati, dukkan su na kawo matsin lamba da juriya da sabuwar gwamnati ke bukatar yi. A wannan yanayin da ake ciki, Li Keqiang ya nuna aniyyarsa, ta fuskantar jarrabawa da zurfafa yin gyare-gyare. Ana da imanin cewa, sabuwar gwamnatin kasar Sin za ta shugabanci jama'arta ta hanyar karfafa yin gyare-gyare, da neman wata sabuwar hanya ta cimma burin samun farfadowar kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China