in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufar hada-hadar kudi don hana hauhawar farashin gidaje
2013-03-14 17:13:17 cri






A ranar 13 ga wata, a nan birnin Beijing, shugaban Baitulmalin kasar Sin wato bankin tsakiya ta kasar Zhou Xiaochuan ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufar kudi yadda ya kamata, sannan kuma za ta dauki kwararan matakai don daidaita farashin kayayyaki da hana hauhawar farashin kayayyaki. Game da hauhawar farashin gidaje da aka samu a kwanan baya, Mr. Zhou ya ce, nan gaba, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai, don cimma burin shawon kan hauhawar farashin gidaje.

A gun taron manema labaru da aka yi a cibiyar yada labaru na taron cikakken zama na farko na majalisar wakilan jama'a karo na 12, lokacin da shugaban bankin tsakiya na kasar Sin Zhou Xiaochuan ke zantawa da manema labaru. Ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta bayar da burin da ta saka a gaba, wato za a samu saurin karuwar tattalin arziki da yawansa zai kai kashi 7.5 cikin 100 a bana, kana kuma za a daidaita yawan saurin karuwar farashin kayayyakin da jama'a suka saya wato CPI zuwa kashi 3.5 cikin 100. Ya kara da cewa, an yi kiyasta cewa, za a samu saurin karuwar M2 wato yawan kudaden da aka yi amfani da su da yawan kudaden ajiya a bankuna da yawansu zai kai kashi 13 cikin 100. Game da wannan, Mr. Zhou ya ce, game da burin da Sin ta saka a gaba, Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufar hada-hadar kudi yadda ya kamata, don cimma burin samun karuwar tattalin arziki, da hana hauhawar farashin kayayyaki. Ya ce,"Bisa kididdigar da aka samu, an ce, idan aka kwatanta burin samun saurin karuwar M2 wato yawan kudaden da aka yi amfani da su, da kudaden ajiya a bankunan kasar na kashi 13 cikin 100, ya yi kasa da adadin da aka samu a bana, abin da ya nuna cewa, za a ci gaba da tabbatar da farashin kayayyaki, haka kuma yanzu, ana kokarin aiwatar da manufofin kudin kasar yadda ya kamata.

Yanzu, yawan kudaden da aka yi amfani da su da yawan kudaden ajiya ya kai kimanin RMB biliyan dubu 100, kuma abin da ya ninka sau 2 bisa na yawan kudin da aka samu wajen samar da kayayyaki wato GDP na bara, sabo da haka ne, ya sa akwai damuwa cewa, wannan zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki cikin dogon lokaci. Game da wannan, Zhou Xiaochuan ya yi bayanin cewa, yawan kudin ajiya da jama'ar Sin suka adana yana da yawa a duniya. Yanzu, jimillar kudaden da Sin ta samar ba za ta kawo hauhawar farashin kayayyaki ba. Ya ce, "Yawan kudaden ajiya da jama'ar Sin suka adana ya yi yawa, nan gaba, idan muka iya daidaita saurin karuwar M2, ba za a fuskanci matsalar hauhawar farashin kayayyaki ba."

Yayin da aka tabo batun samun hauhawar farashin gidaje a birane da dama, Mr. Zhou ya ce, nan gaba, Sin za ta ci gaba da daukar matakai, don cimma burin hana hauhawar farashin gidaje, ya ce, "Da ma, mun aiwatar da manufar daidaita farashin gidaje, alal misali, mun kara yawan kason kudi na farko da aka biya don sayen gida, gami da yawan ruwan bashi da aka bayar, kuma nan gaba, za a ci gaba da kyautata manufofi don daidaita farashin gidaje.

Kwanan baya, wasu kasashe sun aiwatar da manufar sassauta bakin aljihu don sa kaimi ga raya tattalin arziki, cikinsu har da kasar Japan, ko wannan matakin da aka dauka zai kawo tasiri game da tattalin arziki na kasar Sin, wannan batun ya zama wani abun da ya fi daukar hankalin jama'a a gun taron manema labaru. Game da wannan batu, mataimakin shugaban bankin tsakiya na kasar Yi Gang ya ce, yana fatan manyan kasashe G20 za su cika alkawarin da suka dauka, don magance samun rage darajar kudi da gangan don yin takara da sauran kasashe. Ya ce,"Ana fatan kasashen duniya za su aiwatar da manufa bisa daidaiton da aka cimma wa tsakaninsu a gun taron G20, don magance gamu da matsala sakamakon daukar matakan sassauta bakin aljihun, da kuma irin illar da za a kawo wa kasuwannin hada-hadar kudi ta duniya. A sa'i daya kuma, yayin da kasar Sin take yin la'akari da manufarta, ita ma, dole ne ta yi la'akari da wannan batu, da tsara matakan da za a dauka don magance wannan batu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China