Zhou Xiaochuan ya yi wannan furuci ne yayin wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana a cibiyar watsa labarai a taro na farko na majalisar wakilai na 12 na jama'ar kasar Sin.
Shugaban babban bankin jama'ar kasar sin ya yi bayanin cewa, bankin ya na sa ido kan ma'aunin CPI, kuma yana shirin ba da tabbaci ga farashin kayayyaki ta hanyar daukar manufar kudi da sauran matakai da suka dace da kuma hana hauhawar farashin kayayyaki ba bisa shiri ba.
A yayin taron, Pan Gongsheng, mataimakin shugaban babban bankin kasar Sin ya ce, yawan basusukan da suka salwanta a bankunan kasar Sin daga cikin dukkan basusukan da aka ci, da kuma yawan basusukan da suka salwanta ba su da yawa, haka kuma an nuna tabbaci kan kadarorin bankunan kasar Sin. (Amina)