in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi murnar rufe cikakken zama na 1 na CPPCC
2013-03-12 20:08:43 cri
A jaridar People's Daily ta kasar Sin da za a wallafa a ranar Laraba 13 ga wata, za a wallafa sharhin edita mai take "kama sabuwar hanyar da za a iya kaiwa ga bude sabon yanayi" don murnar rufe cikakken zama karo na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC na 12.

Wannan sharhin edita ya ce, a yayin taron, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na kasar su da mambobi masu ba da shawara sun tattauna harkokin dake shafar yadda za a kara bunkasa kasar Sin, inda mambobi masu ba da shawara na majalisar suka yi kokari sosai wajen tattauna harkokin siyasa da kuma samar da shawarwarinsu don sauke nauyin dake wuyansu.

Wannan sharhin edita ya kara da cewa, shimfida dimokuradiyya tsakanin al'umma yana da muhimmanci matuka ga tsarin gurguzu, kuma muhimmin abu ne da ba za a iya maye shi ba ga tsarin siyasa na kasar Sin. Ko majalisun ba da shawara kan harkokin siyasa za su iya bayar da gudummawarsu a fannonin tattaunawar harkokin siyasa, sa ido ta hanyar dimokuradiyya, tattauna da kuma daidaita batutuwan siyasa ko a'a wannan batu yana da muhimmanci sosai kan yadda ake alamta ingancin tsarin gurguzu na dimokuradiyya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China