in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu na ganin cewa, bankin cigaban BRICS zai kasance a Afrika
2013-03-12 10:44:45 cri

Gwamnatin Afrika ta Kudu na da imanin da rashin fargaba cewa, bankin cigaban BRICS, da ake shirin kafawa zai kasance a nahiyar Afrika, a cewar wani jami'in gwamnatin kasar a ranar Litinin.

Ministar Afrika ta Kudu dake kula da huldar kasa da kasa, Maite Nkoana-Mashabane ta bukaci goyon bayan shugaba Zuma domin ganin wannan banki ya tsaya a Afrika ta Kudu.

Zaman taro karo na 5 na kasashen BRICS zai gudana cikin wannan wata a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu, bisa taken 'BRICS da Afrika, dangantakar samun cigaba, dunkulewa da cigaban masana'antu'.

A cewar madam Nkoana-Mashabane, zai kasance abu mai muhimmanci idan Afrika ta kudu ta samu wannan dama na samun bankin cigaban BRICS a kasarta. Ana zaton cewa, a yayin da shugaba Jacob Zuma ya halarci taron BRICS a kasar Indiya a cikin watan Maris da ya gabata, aikinsa shi ne na kawo wannan banki gida. Haka kuma ministar ta nuna cewa, bankin zai taimakawa Afrika a cikin tsare-tsaren ayyukan gine-gine.

Haka shi ma babban manajan ''Business Unity SA'', Nomaxabiso Majokweni ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Litinin cewa, wannan banki da kasashen BRICS suke fata zai karfafa cigaba da zuba jari a cikin kasashe mambobi da kuma sauran kasuwannin masu tasowa, haka zai kasance wani inkiya na kawo sauye-sauye a cikin hukumomin kudi na kasa da kasa. Kuma wata riba ta kai tsaye ga Afrika ta Kudu a cikin tsarin cigaban gine-gine, da zai taimakawa gwamnati cimma wasu muhimman maradun samun cigaba da ta sanya a gaba, in ji mista Majokweni. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China